Yan sanda sun kama kasurgumin mai garkuwa da mutane a Katsina

Yan sanda sun kama kasurgumin mai garkuwa da mutane a Katsina

- Hukumar yan sandan jihar Katsina tace ta kama wani da ake zargin mai garkuwa da mutane ne, Ibrahim Muwange

- Dan ta'addan na cikin jerin wadanda yan sanda ke nema ruwa a jallo

- Yana daga cikin yan ta’addan da suka addabi mutanen Danmusa, Malumfashi, Safana da kuma Batsari

Rundunar yan sandan jihar Katsina tace ta kama wani da ake zargin mai garkuwa da mutane ne, Ibrahim Muwange wanda ya addabi garuruwan da ke kananan hukumomi hudu a jihar.

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa daga jami’in hulda da jama’a na rundunar, Isa Gambo wanda aka ba manema labarai a ranar Litinin, 4 ga watan Fabrairu a Katsina.

Sanarwar ya bayyana cewa, an kama dan ta’addan wanda ke cikin jerin sunayen da yan sanda ke nema ruwa a jallo da dadewa a ranar Asabar a Dayi da ke karamar hukumar Malumfashi, biyo bayan wani bayani.

Yan sanda sun kama kasurgumin mai garkuwa da mutane a Katsina
Yan sanda sun kama kasurgumin mai garkuwa da mutane a Katsina
Asali: Depositphotos

“Mai laifin na cikin jerin wadanda rndunar ke nema ruwa a jallo wadanda ked a alaka da kes da dama irin su fashin shanu, garkuwa da mutane, fashi da makami da kuma kisan kia.

“Yana daga cikin yan ta’addan da suka addabi mutanen Danmusa, Malumfashi, Safana da kuma Batsari dukkansu kananan hukumomi ne a jihar,” inji sanarwar.

KU KARANTA KUMA: Tashin hankali yayinda rikici ya kaure a tsakanin magoya bayan APC da PDP a Delta

Ya ci gaba da cewa a lokacin binciken yan sanda an gan wani bindigar AK 47 a hannunsa.

Sanarwar ya kara da cewa za a kai mai laifin kotu ba tare da bata lokaci ba.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel