Yanzunnan: Dandanzon jama'a sun halarci kaddamar da yakin zaben Buhari a Gombe

Yanzunnan: Dandanzon jama'a sun halarci kaddamar da yakin zaben Buhari a Gombe

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da yakin zabensa a babban filin wasanni na jihar Gombe

- Shugaban kasar, wanda ya samu rakiyar mataimakinsa, Yemi Osinbajo da kuma sauran jiga jigan jam'iyyar APC ya isa filin wasannin ne da misalin karfe 11:57 na safiyar Asabar

- Sai dai, rahotanni sun bayyana cewa hayaniyar jama'a ta hana bada damar sauraron jawaban da ake gabatarwa a wajen taron

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da yakin zabensa a babban filin wasanni na Gombe, domin neman amincewar jama'ar jihar, akan kad'a masa kurinsu a zaben kujerar shugaban kasa da zai gudana a ranar 16 ga watan Fabrerun da muke ciki.

Shugaban kasar, wanda ya samu rakiyar mataimakinsa, Yemi Osinbajo da kuma sauran jiga jigan jam'iyyar APC ya isa filin wasannin ne da misalin karfe 11:57 na safiyar Asabar, 2 ga watan Fabreru, 2019.

Shigar shugaban kasa Buhari filin wasannin ke da wuya, dandanzon jama'ar da suka taru a filin wasannin, suka dau sowa da tafi, tare da nuna tsantsar goyon bayansu ga tazarcen shugaban kasar.

KARANTA WANNAN: Da duminsa: Shugaban APC a Adamawa da aka sace ya samu 'yanci yanzu

Yanzunnan: Dandanzon jama'a sun halarci kaddamar da yakin zaben Buhari a Gombe
Yanzunnan: Dandanzon jama'a sun halarci kaddamar da yakin zaben Buhari a Gombe
Asali: UGC

Sai dai, rahotanni sun bayyana cewa, daga shi kansa shugaban masu gabatar da jawabin tsare tsare a taron (MC) da jami'an jam'iyyar APC, sun gaza dai-daita dandazon jama'ar domin samun sararin yin jawabi ko kuma basu damar sauraron jawaban mahalarta taron.

Cikakke labarin na zuwa...

A wani labarin kuma; Rahotannin da Legit.ng ta samu yanzu na nuni da cewa masu garkuwa da mutane, sun sako shugaban jam'iyyar APC na jihar Gombe, wanda suka sace awanni 11 kafin zuwan shugaban kasa Muhammadu Buhari kaddamar da yakin zabensa a jihar. A yanzu dai shugaban jam'iyyar ya na tare da iyalinsa cikin koshin lafiya.

Sakataren watsa labarai na jam'iyyar APC a jihar Gombe, Mohammed Abdullahi ya tabbatar da cewa shugaban jam'iyyar APC na karamar hukumar Demsa da wasu masu garkuwa da mutane suka sace ya samu 'yanci a yanzu.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta: Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel