PDP ta yi babban kamu a jihar Kebbi inda wani jigon APC da wasu 3,510 suka sauya sheka zuwa jam’iyyar

PDP ta yi babban kamu a jihar Kebbi inda wani jigon APC da wasu 3,510 suka sauya sheka zuwa jam’iyyar

- Wani jigon APC Mainasara Sajo ya sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP a jihar Kebbi

- Ya sauya shekar ne tare da wasu mambobin jam'iyyar 3,510

- Sun bayyana cewa sun bar APC ne saboda rashin adalcin da aka yi masu aa lokacin zaben fidda gwani

Wani tsohon sakataren gidan gwamnati, Mainasara Sajo, tsoffin shugabannin kananan hukumomi 10 da hadimansu sun bar jam’iyyar All Progressive Congress (APC) tare da magoya bayansu inda suka koma jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a karamar hukumar Suru da ke jihar.

Sajo wanda yayi a matsayin sakataren gidan gwamnati a karkashin shugabancin Saidu Dakingari ya sanar da sauya shekar nasa daga APC zuwa PDP a wajen gangamin kamfen din dan takarar gwamna na PDP, Sanata Isa Galaudu a yankin Dakingari da ke jihar a ranar Alhamis, 31 ga watan Fabrairu.

PDP ta yi babban kamu a jihar Kebbi inda mambobin APC 3,510 suka sauya sheka zuwa jam’iyyar

PDP ta yi babban kamu a jihar Kebbi inda mambobin APC 3,510 suka sauya sheka zuwa jam’iyyar
Source: UGC

Yace daga shi har mabiyansa sun bar APC ne saboda rashin adalcin da aka yi masu aa lokacin zaben fidda gwani.

“Ba a yi mana adalci ba a lokacin zaben fidda gwani, an nuna son kai karara sannan aka gudanar da zaben ba bisa ka’ida ba,” inji shi.

KU KARANTA KUMA: Yanzu yanzu: Yan bindiga sun kai farmaki ga tawagar 'yan sanda, sun kashe ASP a Delta

Sauran manyan yan siyasar da suka bar APC a lokacin kamfen din sun bayyana cewa za su tabbatar da nasarar PDP a yankin saboda damar da jam’iyyar tab a yankin na samar da dan majalisar wakilai da sanata a zabe mai zuwa.

Dan takarar gwamnan PDP a jihar, Sanata Galaudu ya zargi gwamnatin APC a jihar Kebbi da rashin kokari da kuma gaza cika alkawaran da ta daukarwa mutanen jihar a lokacin kamfen.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel