Jigawa: Buhari zai tarbi tsohon gwamnan jihar, yan PDP, da kuma yan takarar gwamna da suka sauya sheka

Jigawa: Buhari zai tarbi tsohon gwamnan jihar, yan PDP, da kuma yan takarar gwamna da suka sauya sheka

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai ziyarci Jigawa a gobe Asabar don kaddamar da kamfen dinsa a jihar

- Buhari zai kuma tarbi manyan yan siyasar jihara suka sauya sheka zuwa jam'iyyar APC daga jam'iyyun adawa

- Ciki harda tsoffi kwamishinoni da yan takarar gwamna

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Asabar, 2 ga watan Fabrairu zai ziyarci jihar Jigawa domin ci gaba da gangamin kamfen dinsa.

Ana sanya ran cewa Shugaban kasar zai tarbi tsohon gwamnan jihar Jigawa Ali Sa’ad Birnin-Kudu, dan takarar gwamna a jam’iyyar Peoples Democratic Party, PDP, Hon. Tijjani Kiyawa, tsoffin kwamishinoni da suka yi aiki a karkashin gwamnatin Sule Lamido da dubban magoya bayansu.

Jigawa: Buhari zai tarbi tsohon gwamnan jihar, yan PDP, da kuma yan takarar gwamna da suka sauya sheka
Jigawa: Buhari zai tarbi tsohon gwamnan jihar, yan PDP, da kuma yan takarar gwamna da suka sauya sheka
Asali: Twitter

A yayin ziyarar Shugaban kasar zuwa jihar Jigawa zai kaddamar da dan takarar gwamna na APC a zabe mai zuwa, Gwamna Muhammadu Badaru Abubakar wanda ke neman zarcewa a karo na biyu.

KU KARANTA KUMA: APC Gombe ta kammala duk wani shirye-shirye don ziyarar Buhari

Shugaba Buhari zai tarbi dubban masu sauya sheka daga PDP zuwa APC, cikinsu harda tshon kwamishinan aiki da sufuri, Engr. Baba S. Aliyu, tsohn kwamishinan ruwa da ayyuka na musamman, Engr. Abdulkadir Jinjiri Dutse da kuma Hon. Auwalu Harbo.

Sauran sun hada da kwamishinar shari’a da kwamishinar harkokin mata, Barr. Yakubu Rubah da Fatima Widi Jalo. Da kuma yar takarar gwamna a jam’iyyar SDP Hajia Rabi El-leman, sakataren PDP a arewa maso yamma, Yusuf Adamu Babura da sauransu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel