APC Gombe ta kammala duk wani shirye-shirye don ziyarar Buhari

APC Gombe ta kammala duk wani shirye-shirye don ziyarar Buhari

- Jam'iyyar APC a jihar Gombe tace ta kammala duk wasu tsare-tsare don zuwan Shugaban kasa Muhammadu Buhari jihar

- Shugaba Buhari zai ziyarci jihar ne a gobe Asabar, 2 ga watan Fabrairu domin kaddamar da kamfen dinsa a jihar

- Kakakin jam'iyyar yace Buhari zai zai tarbi wasu manyan yan siyasa daga jam’iyyun adawa a goben

Jam’iyyar All Progressive Congress (APC) a jihar Gombe tace ta kammala duk wasu tsare-tsare don zuwan Shugaban kasa Muhammadu Buhari jihar wanda aka shirya zuwan a ranar Asabar, 2 ga watan Fabrairun 2019.

Malam Kabiru Ibn-Mohammed, babban sakataren labarai na APC a jihar ya bayyana hakan ga manema labarai a Gombe a ranar Juma’a, 1 ga watan Fabrairu.

Yace ana sanya ran Shugaban kasar wanda zai z gangamin kamfen dinsa na neman kujerar Shugaban kasa a karo na biyu zai tarbi wasu manyan yan siyasa daga jam’iyyun adawa.

APC Gombe ta kammala duk wani shirye-shirye don ziyarar Buhari

APC Gombe ta kammala duk wani shirye-shirye don ziyarar Buhari
Source: UGC

A cewarsa da zaran Shugaban kasar ya iso zai ziyarci wasu manyan masu tsaki a jihar kamar masarautar sarki da sauransu.

KU KARANTA KUMA: Amfanin kubewa guda 5 a jikin Dan Adam

Yace ba don Shugaban kasar na sn cika wasu manyan sinadarai na damokradiya ba, da ba sai ya zo ba domin yana da cikakken goyon baya daga mutanen Gombe da dadewa.

Jam’iyyar APC a jihar ta roki jama’a da su tabbatar da zaman lafiya a lokacin gangamin inda ta tunatar dasu cewa damokradiyya ba madaci bane.

A wani lamar na daban, mun i cewa Gamayyar kungiyar mabiya addinin kirista a Najeriya watau Christian Association Nigeria (CAN) a takaice sun yi wa Shugaba Muhammadu Buhari wa'azi mai ratsa zuciya game da zabukan gama gari da ake shirin gudanarwa da dukkan fadin kasar nan da 'yan kwanaki.

Kungiyar wadda ta yi masa wa'azain a cikin wata takardar matsaya da ta fitar bayan taron ta na lokaci-zuwa-lokaci da ta gudanar a garin Abuja, tace ya kamata ya san girman alkawari ya tabbatar da gudanar da sahihin zabe domin kaucewa rikici da zubda jini.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel