Wani gwamnan APC a Arewa ya sha ihu wurin gangamin yakin neman tazarcen sa (Bidiyo)

Wani gwamnan APC a Arewa ya sha ihu wurin gangamin yakin neman tazarcen sa (Bidiyo)

Wasu mafusatan matasa sun yi ta yiwa gwamnan jihar Neja dake a shiyyar Arewa ta tsakiya, Alhaji Abubakar Sani Bello ihu yayin da yaje gangamin yakin neman zaben sa a karamar hukumar Rijau ranar Larabar da ta gabata.

Kamar yadda muka samu, faifan bidiyon da ya rika yawo na dauke da matasan ne cikin fushi suna kokarin yiwa gwamnan bore ta hanyar ihu inda suke ishara ga gwamnan cewa karamar hukumar su na matukar bukatar hanya inda suke kiran cewa 'ba hanya'.

Wani gwamnan APC a Arewa ya sha ihu wurin gangamin yakin neman tazarcen sa (Bidiyo)

Wani gwamnan APC a Arewa ya sha ihu wurin gangamin yakin neman tazarcen sa (Bidiyo)
Source: Depositphotos

KU KARANTA: Zan yafewa barayin gwamnati idan na ci shugaban kasa - Atiku

Legit.ng Hausa wadda ta kalli bidiyon ta kuma ga wasu daga cikin 'yan tawagar gwamnan suna kokarin kwantarwa da matasan hankalin suna kokarin hana su yin ihun amma su kuma suka ki ji suka kuma cigaba da ihun su.

Sai dai legit.ng Hausa ba zata iya tabbatar da cewa ko gwamnan wanda yake da dan tazara da matasan yana ta kokarun bayyana manufofin sa ga mahalarta taron ya ji ihun da matasan ke yi ba ko kuma a'a.

Su dai al'ummar karamar hukumar ta Rijau suna cikin mawuyacin hali ne sakamakon lalacewar hanyar garin na Rijau zuwa Kontagora da tayi shekaru da dama da suka shude wadda kuma gwamnan jihar Alhaji Abubakar Sani Bello yayi alkawarin gyara masu a shekarar 2015.

Sai dai kuma kimanin shekaru hudu da wannan alkawarin nasa, mun samu cewa gwamnan bai cika masu ba wanda hakan ne ya hasala matasan.

Ga dai bidyon ihun nan:

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel