Shugaba Buhari yayi alkawarin sake inganta Najeriya a Kano

Shugaba Buhari yayi alkawarin sake inganta Najeriya a Kano

- Shugaban kasa Buhari ya bayyana cewa zai ci gaba da aiki ba ji ba gani domin daukaka kasar Najeriya da kuma wanzar da zaman lafiya a cikinta idan har aka sake zabarsa a karo na biyu

- Buhari yace ya cika alkawaran zaben da ya dauka a shekarar 2015

- Dan takarar na APC ya ci gaba da bayyana cewa anyi tanadi da dama don Najeriya ta tsaya da kafafunta a fannin harkar noma

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa zai ci gaba da aiki ba ji ba gani domin daukaka kasar Najeriya da kuma wanzar da zaman lafiya a cikinta idan har aka sake zabarsa a karo na biyu a zaben ranar 16 ga watan Fabrairu.

Da yake jawabi ga dubban mambobin APC da suka tattaru a filin wasa na Sani Abacha a Kano domin yiwa jirgin kamfen dinsa maraba da zuwa, Shugaban kasar yace ya cika alkawaran zaben da ya dauka a shekarar 2015.

Shugaban kasar yace gwamnatinsa ta cika alkawarinta ta fannin inganta tsaro a fadin kasar, habbaka tattalin arzikin kasar da kuma yaki da cin hanci da rashawa a tsakanin al’umman kasar.

Shugaba Buhari yayi alkawarin sake inganta Najeriya a Kano

Shugaba Buhari yayi alkawarin sake inganta Najeriya a Kano
Source: Facebook

Buhari ya ci gaba da bayyana cewa anyi tanadi da dama don Najeriya ta tsaya da kafafunta a fannin harkar noma.

KU KARANTA KUMA: 2019: APC ta yi babban rashi a Akwa Ibom yayinda manyan jam’iyyar da magoya bayansu suka koma PDP

Ya kuma ce gwaamnatinsa ta yi kokari sosai wajen toshe duk wata kafa da kuma samar da asusu guda na kasa domin hada albarkatun kasar a waje guda.

A nashi bangaren, Shugaban jam’iyyar All Progressive Congress na kasa, Adams Oshiomole yayi watsi da rade-radin cewa jam’iyyar na shirin yin magudin zabe cewa basu bukatar yin magudi a zabe.

A cewarsa, jam’iyyar bata bukatar magudin zabe domin basu da ilimin magudin zabe maimakon haka sun san yadda za su hana jam’iyyar adawa yin magudin zabe.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel