Yanzu Yanzu: Filin wasa na Sani Abacha ya zama babu masaka tsinke tun kafin isowar Buhari filin taro
A yanzu haka Filin wasa na Sani Abacha ya zama babu masaka tsinke tun kafin isowar Shugaban kasa Muhammadu Buhari filin taro.
Shugaban Kasa Buhari dai ya isa jihar Kano a yau Alhamis, 31 ga watan Janairu domin ci gaba da gangamin kamfen dinsa na neman kujerar shugabancin kasar a karo na biyu.

Asali: Facebook
Da isar sa jihar, Shugaban kasar tare da gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje sun garzaya fadar mai martaba sarkin Kano, Muhammad Sanusi domin kwasar gaisuwa.

Asali: Facebook
Shugaban kasar ya samu kyakyawar tarba a fadar Sarki Sanusi.

Asali: Facebook
Ga karin hotuna daga filin taron kamfen din shugaban kasar.

Asali: Facebook

Asali: Facebook
Mun kawo cewa jirgin shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya tashi daga babban filin jirgin Nnamdi Azikwe Abuja zuwa filin jirgin Aminu Kano dake birnin Kano.
KU KARANTA KUMA: Yadda na hana wani tshohon gwamna dawowa kujerarsa – Atiku
Mun samu wannan ne daga bakin hadimin Buhari kan sabbin kafafen yada labarai, Bashir Ahmed, inda yace: "Shugaba ya tashi daga filin jirgin saman Nnamdi Azikwe Abuja zuwa Kano, zai halarci taron yakin neman zabe a babban filin kwallon Sani Abacha."
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT
Asali: Legit.ng