Zuwan Buhari Kalaba: An gwabza kazamin fada tsakanin 'ya'yan jam'iyyar APC

Zuwan Buhari Kalaba: An gwabza kazamin fada tsakanin 'ya'yan jam'iyyar APC

Magoya bayan bangarori biyu da basa ga-maciji da juna da kuma dukkan su ke goyon bayan dan takarar gwamna a jam'iyyar APC a jihar Kuros Riba yayin da shugaba Muhammadu Buhari ya je jihar a cigaba da zagayen gangamin yakin neman zaben da yake yi jiha jiha.

Kamar yadda muka samu, fadan a tsakanin magoya bayan biyu ya kaure ne a daidai lokacin da shugaba Buhari ya dira garin na Kalaba, babban birnin jihar Ribas a kan hanyar sa ta zuwa filin wasa na UJ Esuene ranar Laraba.

Zuwan Buhari Kalaba: An gwabza kazamin fada tsakanin 'ya'yan jam'iyyar APC

Zuwan Buhari Kalaba: An gwabza kazamin fada tsakanin 'ya'yan jam'iyyar APC
Source: Depositphotos

KU KARANTA: Idan na mutu, Buhari ne sila - Ortom

Legit.ng Hausa ta samu cewa magoya bayan da suka gwabza dai sune na Sanata Owan-Enoh wanda ke zaman dan takarar gwamnan jihar da ya samu tikiti da kuma magoya bayan Usani Usani dake zaman minista a gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.

Majiyar mu da lamarin ya faru akan idon sa ya bayyana cewa magoya bayan bangarorin sun yi ta dukan junan su da itace wanda har hakan yayi sanadiyyar raunata magoya bayan dan takarar Gwamnan jihar na APC biyu.

A wani labarin kuma, Wasu fitattun 'yan Najeriya da suka hada da tsohon Sakataren dindin din na majalisar dinkin duniya Cif Emeka Anyaoku da kuma shugaban darikar Katolika ta shiyyar Sokoto Bishop Matthew Kukah sun fadawa Shugaba Buhari gaskiya game da salon mulkin sa.

Da suke gabatar da jawaban su a lokutta daban-daban a wajen bikin cikar jaridar Nigerian Tribune shekaru 70 da kafuwa, fitattun mutanen sun ce maganar gaskiya abubuwa da dama ba su tafiya yadda ya kamata a kasar karkashin jagorancin shugaban kasar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel