Yanzu Yanzu: Kwamishinan Yobe ya ajiye aiki domin zama mataimakin gwamna

Yanzu Yanzu: Kwamishinan Yobe ya ajiye aiki domin zama mataimakin gwamna

- Kwamishinan kasafin kudi da tsare-tsaren tattalin arziki na jihar Yobe, Idi Barde Gubana ya sauka daga matsayinsa

- Hakan ya biyo bayan kudirinsa na yiwa dan takarar gwamna na jam'iyyar APC a jihar mataimakin gwamna

- Ya sha alwashin yin shugabanci na gari idan aka zabe shi a matsayin mataimakin gwamna

Kwamishinan kasafin kudi da tsare-tsaren tattalin arziki na jihar Yobe, Idi Barde Gubana ya sauka daga matsayinsa domin yi wa dan takarar gwamna na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) candidate, Hon. Mai Mala Buni mataimaki.

Ya mika harkokin ma’aikatar zuwa ofishin gwamna a Adamaturu a ranar Laraba, 30 ga watan Janairu.

Yanzu Yanzu: Kwamishinan Yobe ya ajiye aiki domin zama mataimakin gwamna

Yanzu Yanzu: Kwamishinan Yobe ya ajiye aiki domin zama mataimakin gwamna
Source: Depositphotos

Ya bayyana cewa hukuncinsa na takarar mataimakin gwamna tare da tsohon sakataren APC na kasa a zaben ranar 2 ga watan Maris, 2019 ne ya sanya shi yin murabus.

“Na yi sa’a yin aiki a kakashin gwamnatin Gwamna Ibrahim Gaidam a matsayin kwamishina sannan ban yi danasani ba ko kadan saboda an kula da mu da kyau.

KU KARANTA KUMA: Sarakunan gargajiya a Ebonyi sun marawa Buhari baya

“Zan fada ba tare da kowani shakku ba cewa mun yi nasarar gina suna da martaba a ma’aikatar dama jihar,” inji shi.

Ya yaba da dukkan goyon bayan da ma’aikatan ma’aikatar suka bashi sannan yayi alkawarin yin shugabanci na gari idan aka zabe shi a matsayin mataimakin gwamna.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel