Asiri ya tonu: Yadda na murde zaben ANPP a 2003 domin Buhari ya yi nasara - Bafarawa

Asiri ya tonu: Yadda na murde zaben ANPP a 2003 domin Buhari ya yi nasara - Bafarawa

- Attahiru Bafarawa, ya ce shi ne ya murde zaben fitar da gwani na shugaban kasa karkashin jam'iyyar ANPP a zaben 2003 domin ganin Muhammadu Buhari ya ci zaben

- A cewar sa, Okorocha ne ya lashe zaben, inda ya samu nasara a jihohi 27 cikin 36 hadi da babban birnin tarayya Abuja, yayin da Buhari ya samu nasara a jihohi 5 kacal

- Bafarawa ya ce ya baiwa Buhari N5m domin ya rabawa shuwagabannin jam'iyyar na jihohi 36 da sunan sanyawa motocinsu mai idan zasu koma gida

Attahiru Bafarawa, tsohon gwamnan jihar Sokoto, ya ce shi ne ya murde zaben fitar da gwani na shugaban kasa karkashin jam'iyyar ANPP a zaben 2003 domin baiwa Muhammadu Buhari damar lashe zaben.

Buhari ya samu tikitin tsayawa takarar shugaban kasar a karkashin ANPP, amma ya sha kasa a hannun tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo a lokacin babban zaben.

Bafarawa, wanda a lokacin yake rike da mukamin shugaban jam'iyyar na ANPP, ya ce Rochas Okorocha ya shirya samun tikitin shugaban kasar a ANPP biyo bayan wani zaben share fage da aka gudanar kafin babbar zaben fitar da gwani na jam'iyyar.

A cewar sa, Okorocha ne ya lashe zaben, inda ya samu nasara a jihohi 27 cikin 36 hadi da babban birnin tarayya Abuja, yayin da Buhari ya samu nasara a jihohi 5 kacal.

KARANTA WANNAN: Hattara 'yan Nigeria: Martaba da darajar Buhari da kuke gani dodo-rido ce - Obasanjo

Asiri ya tonu: Yadda Bafarawa ya murde zaben ANPP na 2003 domin Buhari ya ci

Asiri ya tonu: Yadda Bafarawa ya murde zaben ANPP na 2003 domin Buhari ya ci
Source: Depositphotos

Bayanai kan hakan na kunshe ne a cikin wani sabon littafi mai suna, ‘Politics as Dashed Hopes in Nigeria’, wanda Auwal Anwar, PhD, kuma tsohon mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin FCTA daga 2004-2007 ya wallafa.

Littafin ya yi bayani dalla dalla kan harkokin jam'iyyar CPC wacce Buhari ya assasa domin tsayawa takara a zaben shugaban kasa na 2011 bayan da ya gaza katabus a jam'iyyar ANPP, la'akari da faduwa zaben 2003 da 2007.

A zantawarsa da marubucin littafin, Bafarawa wanda a yanzu mamba ne a jam'iyyar PDP, ya ce: "Na roki shuwagabannin jam'iyyar na jihohi da su canja ra'ayinsu na zabar wani, su hakura su zabi Buhari. Na kuma umurci daya daga cikin ma'aikata na, Abdullahi Bida, dan uwan Buba Galadima, da ya baiwa kowannensu N500,000. Daga baya na kira Janar Buhari da ya same ni a dakin saukar gwamnonin jihar Niger, inda na ke zaune. Ya iske ni da misalin karfe 4 na asuba, tare da Sule Hamma.

"Kari akan hakan, na bashi N5m domin ya basu su sanyawa motocinsu mai idan zasu koma jihohinsu. Ya karbi kudin tare da gode mani akan dukkanin dawainiyar da nake yi. Bayan kammala taron ya basu kudin."

Sai dai bayan faduwa zaben 2007, Buhari ya zargi gwamnonin ANPP da cin amanarsa, inda ya fice daga jam'iyyar zuwa CPC.

A yanzu dai ANPP da CPC na daga cikin jam'iyyun da suka hada maja inda suka kafa jam'iyyar APC wacce ta lashe zaben 2015, a wani yanayi mai ban mamaki, na tunkude gwamnatin da ke mulki.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel