Jarimin Soja ya rasa ransa a filin daga ana saura kwanaki daurin aurensa (Hotuna)

Jarimin Soja ya rasa ransa a filin daga ana saura kwanaki daurin aurensa (Hotuna)

Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun!!!

Wani jarimin jami'an hukumar sojin Najeriya mai suna, Isah, ya rasa ransa a yakin Boko Haram ana sauran yan kwanaki kalilan da aurensa.

Legit.ng Hausa ta samu wannan rahoton ne daga shafin wani matashi , Muawiyah Umar, a yanar gizo inda ya bayyana cewa ranan 1 ga watan Febrairu, 2019 aka sanya ranan daurin auren Isah da masoyiyarshi amma Allah bai nufa ba.

Ya yi bayanin yadda Jarumi Isah ya mutu yana gwagwarmaya domin kare kasarsa ta Najeriya da yan ta'addan Boko Haram a garin Buni Yadi, jihar Adamawa.

Jarimin Soja ya rasa ransa a filin daga ana saura kwanaki daurin aurensa (Hotuna)

Isah Soja
Source: Facebook

KU KARANTA: Hotunan da bidiyon yadda mutan jihar Abiya suka tarbi shugaba Muhammadu Buhari

Yace: "An saka Ranar daurin Auren Shi 01/02/2019, yau sauran kwana bakwai Allah ya dauki Ransa.

Wannan jajirtaccen, Hazikin jarumin soja Mai Suna isah A. ya rasa ranshi a fagen gumurzu da Yan ta'addan Boko Haram A wani Hari da suka kai A garin Buni yadi dake jihar Yobe .

Mun Addu'ar Allah Ya jikansa Da Rahama Yayi masa sakayya da gidan Aljannah

muna Addu'a sauran sojojin mu Allah ya Kare mana su, Kuma ya Basu nasara Akan Wannan yaki da sukeyi da kungiyar Boko Haram Amin."

Jarimin Soja ya rasa ransa a filin daga ana saura kwanaki daurin aurensa (Hotuna)

Jarimin Soja ya rasa ransa a filin daga ana saura kwanaki daurin aurensa (Hotuna)
Source: Facebook

Mun kawo muku a baya cewa a ranar Lahadi, 20 ga watan Junairu, 2018, rundunar sojin Najeriya sun sami gagarumin nasara kan mayakan Boko Haram yayinda suka kai wata mumunan hari barikin sojoji dake garin Buni-yadi, jihar Yobe.

Mataimakin kakakin rundunar 27 Brigade. Major Nureni Alimi, ya bayyana hakan ne da safiyar Litinin a shafin sadarwa hukumar sojin.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel