Ba saboda kudi nake goyon bayan Atiku ba – Sani Danja

Ba saboda kudi nake goyon bayan Atiku ba – Sani Danja

- Shahararren jarumin nan na masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Sani Musa Danja, ya yi tsokaci akan dalilin da yasa yake goyon bayan Atiku a zabe mai zuwa

- Danja yace yan goyon bayan dan takarar na PDP ne don ra'ayin kansa amma ba wai don kudi ba

- Hakan na zuwa ne bayan abokiyar aikinsu Ummi Zeezee ta aika wa Danja da wasu manyan jaarumai zagi kwando-kwando

Shahararren jarumin nan na masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Sani Musa Danja, ya yi tsokaci akan dalilin da yasa yake goyon bayan tsohon mataimakin Shugaban kasa kuma dan takarar Shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar

A cewar Danja ba wai saboda kudi yake goyon bayan dan Atiku Abubakar ba a zaben da za a gudanar a ranar 16 ga watan Fabrairu.

Jarumin ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da shafin labarai na BBC, inda ya jadadda cewa duk abin da suke yi ra'ayi ne ya sa suke yi.

Ba saboda kudi nake goyon bayan Atiku ba – Sani Danja

Ba saboda kudi nake goyon bayan Atiku ba – Sani Danja
Source: Depositphotos

Dan wasan ya ce kashi 85 cikin 100 na masu goyon Atiku suna yi ne don ra'ayin kansu, "ko kuma gajiya da wannan gwamnati ko kuma neman mafita ko kuma saboda rashin jin dadin abubuwan da suka faru shekara uku da suka wuce," in ji shi.

A baya mun ji cewa tsohuwar ‘yar wasan Hausa Ummi Zeezee ta aika wa wasu daga cikin abokan aikin ta kwando-kwando na ashar tare da barazanar sa a rufe mata su a Abuja.

KU KARANTA KUMA: Karancin albashi: Jihohi 30 sun amince da biyan N30,000 – NLC

Ummi Zeezee ta koka ne cewa Atiku Abubakar ya aiko wa magoya bayan sa da ke farfajiyar finafinan Hausa da kudade masu yawa inda suka ware kan su sannan suka raba kudin ba tare da sun aika mata da kaso mai tsoka ba.

A shifidaddiyar wasika da ta rubuta inda ta jero sunayen wadanda take yi wa raddi da sakon nata ta ce dukkan su sunci sa’ar mahaifiyar ta ce da ta roke ta da ta yi hakuri da yanzu Sani Danja, Fati Muhammed, Zaharaddeen Sani, Alamin Buhari da Darakta Emrana sun dade a garkame a ofishin SSS na Abuja.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Shafin Naij.com Hausa ya koma Legit.ng Hausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel