Hanyoyi 5 da mutum zai bi don hana furfura fitowa a jikinsa

Hanyoyi 5 da mutum zai bi don hana furfura fitowa a jikinsa

A zamanin baya mutanen da suka tsufa aka sani da farin gashi a kai, wato Furfura, said a a zamanin nan da muke ciki abubuwa da dama sun sauya, harma ana iya ganin jarir sabon haihuwa da farin gashi a kai.

Wannan dalili ne yasa wasu masana gudanar da bincike akan billowar furfura a jikin dan adam.

Masanan sun bayyana cewa billowar furfura a jiki ya rabu kashi biyu ne; Akwai wanda nasu halittace daga Allah n fitowa saboda rashin garkuwar jiki mai karfi.

Likitocin sun ce an hallici jikin mutum da garkuwa da suke taimakawa wurin kare mutum daga kamuwa da cututtuka.

Hanyoyi 5 da mutum zai bi don hana furfura fitowa a jikinsa

Hanyoyi 5 da mutum zai bi don hana furfura fitowa a jikinsa
Source: UGC

‘‘Furfura kan fito a jikin mutum musamman yaro karami idan garkuwar jiki nasa bashi da karfin kare shi daga kamuwa da cututtuka.”

KU KARANTA KUMA: ASUU na iya kawo karshen yajin aiki kwanan nan – Gwamnatin tarayya

Ga wasu hanyoyi da ya kamata mutum ya bi domin guje ma samun garkuwar jiki mara karfi:

1. Yawaita cin abincin dake dauke da sinadarin dake karfafa garkuwar jiki kamar su ganye, kayan lambu, madara, kifi, da dai sauransu.

2. Samun isasshiyar hutu a koda yaushe.

3. Yawan damuwa na kawo furfura a jikin mutum, don haka idan mutum na son kaurace ma haka ya zama dole ya daina sanya dauwa a ransa.

4. A yawaita motsa jiki saboda yana taimakawa wajen bunkasa garkuwar jiki.

5. Idan har utum na son rabuwa da furfura toh ya zama dole ya rage ta'ammali da giya, cin abu mai maiko a koda yaushe, kanzon tukunya da dai sauransu.

6. A dunga tsaftace jiki, muhalli da abinci.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel