Kallo-ya-koma-sama: Tsaleliyar budrwa ta haukace jim kadan bayan saurayin ta ya aje ta daga mota

Kallo-ya-koma-sama: Tsaleliyar budrwa ta haukace jim kadan bayan saurayin ta ya aje ta daga mota

Kamar dai yadda karin maganar Hausawa ke cewa, Kallo ya koma sama wai da shurwa ta dauki dan tsako yayin da wata tsaleliyar budurwa ta haukace jim kadan bayan saurayin ta ya aje ta daga mota a jihar Delta dake a shiyyar kudu maso kudancin Najeriya.

Labarin abun al'ajabin dai ya soma ruruwa ne kamar wutar daji a kafafen sadarwar zamani kamar su Fasbuk da sauransu bayan da wata mata da tayi ikirarin lamarin ya auku a gaban idon ta ta saka bidiyon matar a shafin ta.

Kallo-ya-koma-sama: Tsaleliyar budrwa ta haukace jim kadan bayan saurayin ta ya aje ta daga mota

Kallo-ya-koma-sama: Tsaleliyar budrwa ta haukace jim kadan bayan saurayin ta ya aje ta daga mota
Source: UGC

KU KARANTA: Korar Alkalin Alkalai: Buhari yayi daidai inji wata kungiyar Musulmai

Legit.ng Hausa ta samu haka zalika cewa tuni dai jama'a da dama suka cigaba da tofa albarkacin bakin su game da lamarin inda wasu ke ganin kawai saurayin yayi anfani da ita ne wajen yin tsafi da ita.

Matar dai wadda ta wallafa faifan bidiyon mai suna Oboh Matthew ta ce lamarin ya auku ne da safiyar ranar Larabar da ta gabata a unguwar Ughelli.

Haka zalika jama'a da dama dai sun yi anfani da wannan damar inda suka rika ba mata shawara akan su san irin mu'amalar da suke yi da samarin su domin kar su jefa kan su cikin matsalar da za su dade ba su fita ba.

Ga dai bidiyoyin nan da aka wallafa kan matar:

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel