Kayi-dai-dai: Wata kungiyar musulmai ta goyi bayan Buhari kan dakatar da Alkalin Alkalai

Kayi-dai-dai: Wata kungiyar musulmai ta goyi bayan Buhari kan dakatar da Alkalin Alkalai

Kungiyar dake rajin kare hakkokan mabiya addinin musulunci a tarayyar Najeriya Muslim Rights Concern (MURIC) a turance ta bayyana dakatarwar da shugaba Buhari yayiwa Alkalin Alkalai, Mai shari'a Walter Onnoghen a matsayin abun da ya kamata kuma sadda ya kamata.

Shugaban kungiyar ta MURIC, Farfesa Ishaq Akintola shine ya bayyana hakan a ranar Juma'a cikin wata sanarwar manema labarai da ya fitar jim kadan bayan da shugaban kasar ya rantsar da sabon Alkalin Alkalan a fadar sa.

Kayi-dai-dai: Wata kungiyar musulmai ta goyi bayan Buhari kan dakatar da Alkalin Alkalai

Kayi-dai-dai: Wata kungiyar musulmai ta goyi bayan Buhari kan dakatar da Alkalin Alkalai
Source: UGC

KU KARANTA: Buhari yayi sabon nadi mai muhimmaci

Legit.ng Hausa ta samu cewa Farfesa Ishaq ya kara da cewa tuni cin hancin da ya dabaibaye bangaren shari'a ya bata sunan bangaren kuma dole ne idan har za'a farfado da darajar shari'ar to sai an kakkabe dukkan masu cin hanci da rashawar dake cikin sa.

Za ku tuna cewa gwamnatin shugaba Buhari tana tuhumtar Jastis Onnoghen da laifin rashin bayyana wasu kudade a asusun banki shida duk da kasancewarsa ma'aikacin gwamnati.

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta umurci hukumar leken asirin kudaden sata wato Nigerian Financial Intelligence Unit (NFIU) da ta daskarar da asusun bankin shugaban Alkalan Najeriya, Jastis Walter Onnoghen, guda biyar.

Ranar Juma'a kuma mun kawo maku cewa shugaba Muhammadu Buhari ya sallami shugaban alkalan Najeriya, Jastis Walter Onnoghen kuma ya nada Ibrahi Tanko Muhammad a matsayin mukaddashi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel