Wata malama ta shiga matsala saboda kyamar masu sa hijabi a kasar Birtaniya

Wata malama ta shiga matsala saboda kyamar masu sa hijabi a kasar Birtaniya

'Yan majalisa a kasar Birtaniya sun soma aikin tuhumar mai sa ido a wata makarantar Firamare mai suna Amanda Spielman bisa zargin nuna tsana ga 'ya'yan musulmai a makarantar da ke sa hijabi idan ta kai ziyara.

Sai dai da take maida ba'asi, ita Amanda ta musanta tuhumar inda ta ce ita kawai tana yaki ne da tilastawa yaran sa Hijabi da wasu iyayen kan yi musamman idan za su je makarantar.

Wata malama ta shiga matsala saboda kyamar masu sa hijabi a kasar Birtaniya

Wata malama ta shiga matsala saboda kyamar masu sa hijabi a kasar Birtaniya
Source: Twitter

KU KARANTA: Kotu ta yanke hukunci kan tsayawa takarar APC a Zamfara

Legit.ng Hausa ta samu cewa kafin a gayyaci ita Amanda din, wata kungiya mai rajin kare hakkin al'umma ta kai karar ta ga 'yan majalisar inda suka bukaci a binciki ayyukan ta kuma a ja mata kunne.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa turawa da yawa wadanda ba musulmai sukan nuna kyama wata sa'in kuma hadda tsana ga musulmai masu sa hijabi duk kuwa da cewa hakan bai saba ka'ida ba.

A wani labarin kuma, Amurka da Birtaniya sun ce ba sa goyon bayan kowane dan takara daga cikin masu neman shugabancin Najeriya a zaben da za a yi a watan Fabrairun bana.

Amurka ta ce tana sanya ido tare da sauran kasashe kan mutanen da ke katsalandan a harkokin siyasa, ko kuma suke rura wutar muzgunawa 'yan kasa gabanin zaben, ko da lokacin da ake yinsa ko bayan sa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel