Ta-faru-ta-kare: Kotu ta yanke hukunci kan maganar kin shigar APC zabe a Zamfara

Ta-faru-ta-kare: Kotu ta yanke hukunci kan maganar kin shigar APC zabe a Zamfara

Wata babbar kotun gwamnatin tarayya dake zaman ta a garin Abuja ta tabbatar da hukuncin da hukumar zabe mai zaman kan ta ta kasa watau ndependent National Electoral Commission (INEC) ta dauka kan kin saka jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Zamfara zaben 2019.

A yayin da yake yanke hukunci kan karar dake gaban sa, Alkalin kotun Mai shari'a Ijeoma Ojukwu a ranar Juma'a, yace tabbas hukumar zaben ta kasa tayi daidai akan hukuncin da ta dauka na kin karbar sunayen 'yan takara daga APC a jihar ta Zamfara.

Ta-faru-ta-kare: Kotu ta yanke hukunci kan maganar kin shigar APC zabe a Zamfara

Ta-faru-ta-kare: Kotu ta yanke hukunci kan maganar kin shigar APC zabe a Zamfara
Source: Facebook

KU KARANTA: Amurka tayi magana game da goyon bayan 'yan takara a Najeriya

Legit.ng har ila yau ta tsinkayi alkalin Mai shari'a Ojukwu yana cewa matakin da hukumar ta INEC ta dauka yayi daidai don kuwa hakan ne kadai zai iya magance karfe-karfa da shugabanni ke yi tare da katsalandan a harkokin zabukan yankunan su.

Tun farko dai mun samu cewa wasu 'yan jihar ne suka shigar da kara a kotun suna kalubalantar hukumar ta INEC kan kin karbar sunayen 'yan takarkarin su. A cewar su, sasanci jam'iyyar ta APC tayi wajen fitar da 'yan takara a jihar ta Zamfara.

A wqni labarin kuma, Wata kungiya ta jam'iyyar PDP mai suna Diplomatic Youth Movement of Nigeria (DYMN) ta shiga wata hadin gwuiwa da wata kungiyar ta jam'iyyar APC mai mulki mai suna Youth Mobilisation and Sensitisation (CYMS) domin samun nasarar tazarcen shugaba Buhari.

Shugaban kungiyar ta Diplomatic Youth Movement of Nigeria (DYMN), Malam Yunusa Mohammed shine ya sanar da hakan ranar Laraba a garin Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya lokacin da yake zantawa da manema labarai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel