Gaskiyar magana: Babu wata gaba tsakanina da Hadiza Gabon - Nafisa Abdullahi

Gaskiyar magana: Babu wata gaba tsakanina da Hadiza Gabon - Nafisa Abdullahi

- Nafisa Abdullahi ta bayyana cewa babu wata gaba tsakaninta da kowanne jarumi ko jaruma a masana'antarsu ta fim

- Yar wasan fim din Hausan ta yi karin haske kan dangantakarta da jaruma Hadiza Gabo, wadda kowa ya san cewa akwai sabani a tsakaninsu a baya

- A shekarar 2017 ne fitattun jaruman biyu suka yi fada inda wasu rahotanni suka ce har da duka yayin da suke tsakar shirya wani fim

Nafisa Abdullahi, shahararriyar jarumar fina-finan Hausa, ta bayyana cewa babu wata gaba tsakaninta da kowanne jarumi ko jaruma a masana'antarsu ta fin, tana zaune da kowanne jarumi bisa tsarin da shi jarumin yake so su zauna.

Fitacciyar jarumar, ta yi wannan bayanin a cikin wata hira da ta yi da sashen Hausa na BBC a kwanakin baya.

Nafisa ta ce: "Duk wacce ke son zama da ni lafiya lau, to kuwa nima zan zauna da ita lafiya lau, wacce ke da tunani akasin hakan kuwa, to na kan bita da yadda take so."

KARANTA WANNAN: Noma tushen arziki: Yadda Kano ta zama lamba daya wajen samar da tumatur

Gaskiyar magana: Babu wata gaba tsakanina da Hadiza Gabon - Nafisa Abdullahi

Gaskiyar magana: Babu wata gaba tsakanina da Hadiza Gabon - Nafisa Abdullahi
Source: UGC

Yar wasan fim din Hausan ta yi karin haske kan dangantakarta da jaruma Hadiza Gabo, wadda kowa ya san cewa akwai sabani a tsakaninsu a baya, lamarin da har yanzu wasu ke kallo akwai sauran takun saka tsakanin jaruman biyu.

Jarumar ta kuma yi karin haske a kan dangantakarsu da jaruma Hadiza Gabon, wadda suka samu sabani a baya.

Amma a hirarta da BBC, Nafisa ta ce a yagzu sun fahimci juna ita da Hadiza Gabon bayan da suka dauki dogon lokaci ba sa ga maciji.

Nafisa ta ce, "ko da yake ba mu cika haduwa ba, idan dai har mun hadu muna gaisawa."

Ta ce "dama shi zaman duniya idan dai har ana tare to wata rana dole a samu sabani, domin ko harshe da hakori ma su kan saba."

A shekarar 2017 ne fitattun jaruman biyu suka yi fada inda wasu rahotanni suka ce har da duka yayin da suke tsakar shirya wani fim.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel