Ziyarar Buhari: NSCDC ta tsaurara matakan tsaro a jihar Oyo

Ziyarar Buhari: NSCDC ta tsaurara matakan tsaro a jihar Oyo

- Hukumar tsaro ta NSCDC, reshen jihar Oyo tace ta tanadi tsaro domin ganin an gudanar da kamfen din shugaban kasa Muhammadu Buhari cikin lumana

- A gobe Asabar ne dai jirgin yakin neman zaben shugaban kasar zai dira a Ibadan, babbar birnin jihar Oyo

- Kakakin hukumar yace hukumar ta horar da kimanin jami’ai 120 don zabe mai zuwa a jihar, inda ya kara da cewa za a tura yawancnsu domin wanzar da zaman lafiya a lokacin ziyarar shugaban kasar

Hukumar tsaro ta NSCDC, reshen jihar Oyo tace ta tanadi tsaro domin ganin an gudanar da kamfen din shugaban kasa Muhammadu Buhari a cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali yayinda jirgin yakin neman zabensa za ta tunkari Ibadan a ranar Asabar.

Mista Oluwole Olusegun, kakakin rundunar ya bayyana hakan a wata hira da kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) a ranar Juma’a, 25 ga watan Janairu a Ibadan, babbar birnin jihar Oyo.

Ziyarar Buhari: NSCDC ta tsaurara matakan tsaro a jihar Oyo
Ziyarar Buhari: NSCDC ta tsaurara matakan tsaro a jihar Oyo
Asali: Facebook

Olusegun yace “An tanadi isasshen taro domin hana karya doka da oda a lokacin kamfen din shugaban kasa.”

Yace za a tura jami’an NSCDC a wuraren da ya kamata domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

KU KARANTA KUMA: Kamfen din Atiku: ‘Yan daba sun hallaka wani bawan Allah a Kaduna

Olusegun yace hukumar ta horar da kimanin jami’ai 120 don zabe mai zuwa a jihar, inda ya kara da cewa za a tura yawancnsu domin wanzar da zaman lafiya a lokacin ziyarar shugaban kasar.

Kakakin hukumar ya bukaci yan siyasa da magoya bayansu da su gui duk wani abu da ka iya haddasa rikici, inda ya kara da cewa su rungumi zaman lafiya da junansu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel