An garkame wani Malamin addini biyo bayan kamashi yana luwadi da yara 2

An garkame wani Malamin addini biyo bayan kamashi yana luwadi da yara 2

Wata kotu majistri dake zamanta a garin Ikeja na jahar Legas ta bada umarnin garkame wani malamin addinin kirista, Fasto Seyi Alana bayan an gurfanar da shi gabanta akan tuhume tuhume da suka danganci aikata luwadi da wasu kananan yara biyu ta hanyar fyade.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Alkalin kotun, B.O Osunsanmi ne ta bada umarnin a garkame mata Faston ne bayan dansanda mai shigar da kara, ASP Ezekiel Ayorinde ya bayyana mata duka tuhume tuhumen da suke masa.

KU KARANTA; Gwamnatin jahar Kaduna ta gina wata katafaren kamfanin sarrafa nono da madara

Dansandan yace Faston ya aikata laifin ne a tsakanin watan Yuni da watan Nuwamba na shekarar 2018 a gidansa dake unguwar Igbogbo cikin karamar hukumar Ikorodu ta jahar Legas, inda ya sadu da wasu yara su biyu masu shekaru goma sha bakwai bakwai ta dubura.

“Asirin Faston ya tonu ne bayan da iyayen guda daga cikin suka yi ta neman dansu basu ganshi ba, sa’annan sun rasa inda yake, sai da aka tsananyta bincike sa’annan aka gano shi a dakin Faston, a lokacin ne ya bayyana ma iyayensa abinda Faston yayi musu su biyu da abokinsa.” Inji Dansandan.

Jin haka yasa iyayen yaron suka kai karar Faston zuwa ofishin Yansanda, inda suka garzaya zuwa dakin Faston, suka cimimiyeshi, sa’annan suka gurfanar dashi gaban kotu da nufin a nema ma yaran hakkinsu.

Sai dai Faston ya amsa laifinsa, amma ya nemi kotu ta yi masa sassauci, amma Alkalin kotun, B.O Osunsami ta ki amincewa da magiyarsa, inda ta aikashi gidan yarin Kirikiri, sa’annan tace zata saurari shawarar babban mai shigar da kara na jahar kafin ta cigaba da sauraran karar.

Dansanda Ayorinde yace laifin da ake tuhumar faston da aikatawa ya saba ma sashi na 261 na kundin hukunta manyan laifuka na jahar Legas, wanda idan aka tabbatar da laifin akansa, kotu na da ikon daureshi daurin rai da rai.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel