Malam-ka-san-Allah: Abubuwa 5 da ya kamata ku sani game da Sheikh Abubakar Gumi

Malam-ka-san-Allah: Abubuwa 5 da ya kamata ku sani game da Sheikh Abubakar Gumi

An haifi Shaikh Abubakar Mahmud Gumi (R.A) ne a cikin garin Gumi a Jahar Sakkwato a Arewacin Nijeriya, a shekara ta 1340 bayan Hijira dai dai da shekarar Miladiyya 1922.

Mallam ya tashi ne cikin kyakkyawar tarbiyya da natsuwa da tsafta da neman Ilimi karkashin kulawar mahaifin sa (Alkalin Gumi a wancan zamanin). Kuma yayi karance-karance na zaure a majalisi daban-daban na Malaman da suka shahara anan kasar Hausa a wancan lokaci, tare da karatu na nizamiyya daga nan kasar har kasar Sudan da kasar Saudi Arabiya.

Malam-ka-san-Allah: Abubuwa 5 da ya kamata ku sani game da Sheikh Abubakar Gumi
Malam-ka-san-Allah: Abubuwa 5 da ya kamata ku sani game da Sheikh Abubakar Gumi
Asali: UGC

KU KARANTA: Kungiyar PDP ta shiga hadin gwuiwa da APC don tazarcen Buhari

Shaikh Abubakar Gumi mutum ne mai kokarin binciken Al-kurani da Sunna kan hukunce- hukuncen Shari’a, tun daga abin daya shafi Tauhidi, Hadisi,Fikhu da luggar Larabci, wanda karantarwar da yayi ta tabbatar da haka.

Malam yayi rubuce-rubuce masu yawa, kadan daga cikin su akwai:- Wannnan littafi da za mu fara karantarwa wato “Al Akeedatus Saheehah bi Muwaafakatish Shari’ah” Tarjamar Ma’a’nonin Al-kur’ani Mai Girma. Tafsirin Al-kur’ani: “ Raddul Azhaan ilaa Ma’aanil Kur’an”.

Sauran sun hada da Tarjamar littafin Hadisin “Arba’uunan Nawawiy” Littafi mai suna “Manufata” ko (Where I Stand). Wannan littafi ya na da matukar anfani ga sanin tarin siyasar kasar nan data shafi Addini da Mulki, d.s.s Muna fatan Allah (SWT) cikin Rahamar Sa yayi gafara da jin kai da daukaka ga wannan bawa na sa, wanda ya jaddada Da’awah ta Sunna a wannan kasa mai albarka,tun bayan wafatin Shaikh Usman Dan Fodio (RH).

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel