Iyaye mata kuyi hattara: An gano sinadarai masu guba a cikin nafkin din yara

Iyaye mata kuyi hattara: An gano sinadarai masu guba a cikin nafkin din yara

- Rahotanni sun bayyana cewa akwai wasu sinadarai a nafkin din da ake sa wa kananan yara, wadanda za su iya cutar da yaran

- An yi kira ga daukacin masu ruwa da tsaki da a dauki kwararan matakai domin dakile yaduwar irin wadannan nafkin din

- Sai dai rahoton da hukumar lafiyar kasar ta fitar, bai bayyana sunan kamfanin da ke samar da irin nafkin din ba

Wani rahoto daga Hukumar lafiya ta kasar Faransa Anes, na nuni da cewa akwai wasu sinadarai a nafkin din da ake sa wa kananan yara, wadanda za su iya cutar da yaran kamar sinadarin glyphosate.

Wannan rahoton ya biyo bayan wasu gwaje-gwaje da hukumar ta gudanar, wadanda suka bayyana irin hadarin da sinadaran suke dauke da su ga lafiyar dan Adam. Hukumar Lafiyar ta ce, wannan shi ne karon farko da ta gudanar da gwaji a kan irin wadannan abubuwa.

KARANTA WANNAN: Babbar magana: APC ta sanya kyauta mai tsoka ga akwatin da yafi tarawa Buhari kuri'u a Filato

Iyaye mata kuyi hattara: An gano sinadarai masu guba a cikin nafkin din yara

Iyaye mata kuyi hattara: An gano sinadarai masu guba a cikin nafkin din yara
Source: Twitter

Hukumar ta ce, sanyawa kananan yara musamman ma jarirai wannan nafkin din, na da hatsarin gaske garesu, inda ta yi kira ga daukacin masu ruwa da tsaki da a dauki kwararan matakai domin dakile yaduwar irin wadannan nafkin din.

Ministan lafiyar kasar ta Faransa Agnès Buzyn, ya ce ana daukar kwakkwaran mataki wajen hana sayar da irin wadannan nafkin din, sai dai ya ce ba duka nafkin din ne ke da sinadarin gubar ba.

A don haka inji ministan, ba bu laifi iyaye su ci gaba da sanya wa yaransu nafkin din, amma a rinka kula sosai da irin nafkin din.

Sai dai rahoton da hukumar lafiyar kasar ta fitar, bai bayyana sunan kamfanin da ke samar da irin nafkin din ba.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel