Bauchi: Dogara da jam'iyyu 6 sun daura damarar tunkude gwamnatin M.A Abubakar

Bauchi: Dogara da jam'iyyu 6 sun daura damarar tunkude gwamnatin M.A Abubakar

- Yakubu Dogara, tare da hadin guiwar jam'iyyun siyasa 6, sun daura damarar tunkude gwamnatin Gwamna Muhammadu Abdullahi Abubakar na jihar Bauchi

- Alhaji Mohammed Bello Kirfi, ya ce wannan matakin ya biyo bayan gazawar gwamnatin APC a jihar wajen gudanar da wani abun kirki tsawon shekaru hudu

- Shi kuwa Dogara ya ce, babu abun da gwamna Abubakar yake yi illa daukar nauyin yan bangar siyasa domin tsaron fastoci da alluran takararsa

Akalla jam'iyyun siyasa 6 tare da hadin guiwar wasu masu ruwa da tsaki a siyasar jihar Bauchi karkashin jagorancin kakakin majalisar wakilan tarayya, Yakubu Dogara, sun hada wata kungiyar gamayya domin tunkude gwamnati mai ci a jihar ta Muhammadu Abdullahi Abubakar.

Da yake jawabi ga manema labarai a ranar Lahadi a sakatariyar 'yan jarida ta kasa reshen jihar Bauchi NUJ, wanda ya shirya taron, Alhaji Mohammed Bello Kirfi, ya ce wannan matakin ya biyo bayan kyakkyawan nazari da suka yi na gazawar gwamnatin APC a jihar wajen gudanar da wani abun kirki tsawon shekaru hudu.

KARANTA WANNAN: Da dumi dumi: Jihar Yobe ta shirya karbar bakuncin shugaban kasa Buhari

Gwamnan jihar Bauchi: Muhammad Abdullahi Abubakar
Gwamnan jihar Bauchi: Muhammad Abdullahi Abubakar
Asali: Depositphotos

Jam'iyyun da suka hade waje daya, sun hada da wani tsagi na jam'iyyar APC, jam'iyyar PDP, PRP, ACD, PDM da kuma jam'iyyar GPN.

Kirfi da yake karanta wata sanarwa da ya sanyawa hannu, tare da kakakin majalisar wakilan tarayyar Dogara, Sanata Bala Muhammed, Dr Yakubu Lame, Farfesa Ali Pate, Alhaji Adamu Jumba, Sanata Abdul Ningi, Sanata Bala Tela, Sanata Nazif Gamawa, Sanata Isa Hamma Misau, da sauran 'yan siyasa da shuwagabannin al'umma, ya ce ganin kifewar gwamnatin M.A Abubakar a zabe mai zuwa wani aikine da zasu tabbata ya kammala.

Kakakin majalisar wakilan tarayya: Rt. Hon. Yakubu Dogara
Kakakin majalisar wakilan tarayya: Rt. Hon. Yakubu Dogara
Asali: Twitter

A nashi jawabin, kakakin majalisar wakilan tarayya, Yakubu Dogara, ya kalubalanci gwamnan jihar Bauchi, Muhammad Abdullahi Abubakar akan irin almubazzarancin da yake yi da dukiyar jihar wajen yin allunan talla da kuma hada 'yan bangar siyasar da ke ganin fastoci da allunan tallar sa.

Dogara yayi ikirarin cewa Gwamna Abubakar yayi babban kuskure na tunanin cewa zai iya sayen 'yan siyasar jihar da kudi, yana mai cewa babu wani dan siyasa mai hankali da zai hada hannu da gwamnan duba da irin ta'asar da tafka a gwamnatinsa.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel