Zaben 2019: An gano sabuwar hanyar da Atiku ya shirya tafka gagarumin magudi

Zaben 2019: An gano sabuwar hanyar da Atiku ya shirya tafka gagarumin magudi

Kungiyar nan dake goyon bayan tazarcen Shugaba Muhammadu Buhari a zabukan 2019 da tafi maida hankali musamman a fannin yada labarai watau Buhari Media Organisation (BMO) a turance ta bankado wani sabon salon magudi da suka ce Atiku da PDP sun shirya yi.

A cikin wata sanarwar manema labarai da shugabanta da kuma Sakataren kungiyar suka fitar, sun bayyana cewa jam'iyyar ta adawa da dan takarar ta sun ware makudan kudade domin daukar nauyin magoya bayan su don ganin sun samu shiga cikin ma'aikatan zaben da za'a yi.

Zaben 2019: An gano sabuwar hanyar da Atiku ya shirya tafka gagarumin magudi

Zaben 2019: An gano sabuwar hanyar da Atiku ya shirya tafka gagarumin magudi
Source: Facebook

KU KARANTA: Cincirindon mutanen da suka tarbi Buhari a Benin

Legit.ng Hausa ta samu cewa kungiyar har ila yau ta yi kira ga hukumar zaben mai zaman kanta ta kasa da ta sa ido sosai tare da zakulo wadannan mutanen don tabbatar da samun nasarar zabukan na 2019.

Haka zalika kungiyar ta kuma shawarci sauran 'ya'yan jam'iyyar ta APC da suma su zage damtse don ganin ba'a yi masu sakiyar da ba ruwa ba.

A wani labarin kuma, Wata babbar kotun gwamnatin tarayya dake zaman ta a garin Abuja ta tabbatar da hukuncin da hukumar zabe mai zaman kan ta ta kasa watau ndependent National Electoral Commission (INEC) ta dauka kan kin saka jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Zamfara zaben 2019.

A yayin da yake yanke hukunci kan karar dake gaban sa, Alkalin kotun Mai shari'a Ijeoma Ojukwu a ranar Juma'a, yace tabbas hukumar zaben ta kasa tayi daidai akan hukuncin da ta dauka na kin karbar sunayen 'yan takara daga APC a jihar ta Zamfara.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng News

Tags:
Mailfire view pixel