Duniya juyi-juyi: Sabon Sifeto Janar ya karbi tuta hannun IGP Idris

Duniya juyi-juyi: Sabon Sifeto Janar ya karbi tuta hannun IGP Idris

Duniya juyi-juyi take, an waye gari tsohon sifeto janar na hukumar yan sanda, Ibrahim Kpotum Idrs, ya sauka daga ragamar mulkin hukumar yan sandan Najeriya kuma ya mikawa magajinsa, sabon sifeto, Adamu Mohammad, ragamar.

Mun kawo muku a baya cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya amince wa Abubakar Adamu Mohammed ya zama sabon shugaban rundunar 'yan sanda ta kasa, kamar yadda jaridar Premium Times ta ce majiyar ta a fadar shugaban kasa ta tabbatar mata.

A yammacin yau, Litinin, ne shugaban rundunar 'yan sanda mai barin gado, Ibrahim Idris, ya ziyarci shugaba Buhari, ziyarar da majiyar 'yan sanda ta ce ta zama al'ada ga duk shugaban rundunar da zai bar aiki.

"Muna da sabon shugaban rundunar 'yan sanda," wani babban jami'in dan sanda ya shaidawa Premium Times a daren yau. "Tuni Ibrahim Idris ya koma gida, ya kwashe kayansa daga gidan gwamnati, yanzu muna jiran kawai ya mika mulki ne," jami'in ya tabbatar.

A ranan Talata, an yi bikin mika tuta da karban tuta tsakanin tsohon sifeton da sabon sifeton a sheklwatar hukumar yan sanda ta kasa dake Louis Edet House, birnin tarayya Abuja.

Legit.ng ta garzaya hedkwatan domin kawo muku yadda bikin ya gudana cikin hotuna:

Duniya juyi-juyi: Sabon Sifeto Janar ya karbi tuta hannun IGP Idris
Sabon sifeton yayinda yake karban tuta hannun tsohon
Asali: Original

Duniya juyi-juyi: Sabon Sifeto Janar ya karbi tuta hannun IGP Idris
Sabon sifeton
Asali: Original

Duniya juyi-juyi: Sabon Sifeto Janar ya karbi tuta hannun IGP Idris
IGP Idris bayan karewar wa'adinsa
Asali: Original

Duniya juyi-juyi: Sabon Sifeto Janar ya karbi tuta hannun IGP Idris
Duniya juyi-juyi: Sabon Sifeto Janar ya karbi tuta hannun IGP Idris
Asali: Original

Duniya juyi-juyi: Sabon Sifeto Janar ya karbi tuta hannun IGP Idris
Sabon Sifeto Janar yayinda yake jawabi ga manema labarai
Asali: Original

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel