Bango ya tsake: Kowa ya zabi gwanin sa, kungiyar Izala ba ta siyasa bace - Sheikh Gumi

Bango ya tsake: Kowa ya zabi gwanin sa, kungiyar Izala ba ta siyasa bace - Sheikh Gumi

Daya daga cikin malaman kungiyar Izala a Najeriya, Dakta Ahmad Mahmud Gumi ya ce kowane dan kungiyar na da ikon ya zabi gwanin sa inda maslahar sa take domin kungiyar Izala ba ta siyasa bace.

Dakta Gumi ya bayyana hakan ne a cikin daya daga karatuttukan da yake gabatarwa a masallacin sultan Bello, garin Kaduna a ranar Asabar 12/01/2019 inda ya ja hankalin dukkan Ahlussunnah akan kada su bari wasu mutane su yaudare su da cewar ga wanda zasu zaba.

Bango ya tsake: Kowa ya zabi gwanin sa, kungiyar Izala ba ta siyasa bace - Sheikh Gumi
Bango ya tsake: Kowa ya zabi gwanin sa, kungiyar Izala ba ta siyasa bace - Sheikh Gumi
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: Dalilin da ya sa Dino Melaye ke shan wahala hannun Buhari - Saraki

"Kowa ya duba inda maslahar duniyar sa take ya zabi wanda ya ke so. Kada ku bari wasu fake da wata gararinsu su ce ku zabi wani. Ku duba halayen da zasu iya daidaita wannan kasa da al'ummar ta.

"Aikin izala ba na siyasa ba ce, aikin tabbatar da sunnah ne. Malam Abubakar Mahmud Gumi ya bar wannan kungiyar a hannun wasu dattijai. Son zuciya ne kawai ya hana kungiyar ta hadu. In Sha Allah nan ba da jimawa ba kungiyar zata dawo kan turbarta aka daura ta." Inji shi.

Daga karshe kuma ya ya ce kungiyoyin Izala da Darika su ji tsoron Allah kada su bari fitinar da ta samu shi'a ta same su inda yace su ba zasu bari a bata wannan kungiya ba saboda ikhlasin wanda suka kafata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel