Tsohon bulaliyar majalisar Sokoto, tsoffin shugabannin karamar hukuma 3, da wasu 20,687 sun bar PDP zuwa APC

Tsohon bulaliyar majalisar Sokoto, tsoffin shugabannin karamar hukuma 3, da wasu 20,687 sun bar PDP zuwa APC

- Wani tsohon bulaliyar majalisar dokokin jihar Sokoto, Alhaji Bello Yahaya Wurno ya sauya sheka daga PDP zuwa APC

- Wurno, tsoffin shugabannin karamar hukuma 3, da wasu 20,687 sun koma APC ne a ranar Asabar

- Tsohon mai ba Aminu Tambuwal shawara na musamman ma ya sauya sheka zuwa jam’iyya mai mulki

Wani tsohon bulaliyar majalisar dokokin jihar Sokoto, Alhaji Bello Yahaya Wurno ya sauya sheka daga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki gabannin zaben 2019.

Tsoffin shugabannin karamar hukumar Rabah uku, tsohon mai ba Aminu Tambuwal shawara na musamman da wasu mambobin babbar jam’iyyar adawa 20,687 sun sauya sheka daga babbar jam’iyyar adawa zuwa APC, jarifdar Nigerian Tribune ta ruwaito.

Legit.ng ta tattaro cewa mambobin PDP, wadanda suka bar jam’iyyar adawar a ranar Asabar, 12 ga watan Janairu sun samu tarba a APC a wajen kaddamar da kamfen din jihar Sokoto na yankin yammacin kasa a garuruwan Wurno da Rabah.

Tsohon bulaliyar majalisar Sokoto, tsoffin shugabannin karamar hukuma 3, da wasu 20,687 sun bar PDP zuwa APC
Tsohon bulaliyar majalisar Sokoto, tsoffin shugabannin karamar hukuma 3, da wasu 20,687 sun bar PDP zuwa APC
Asali: UGC

Alhaji Bello Yayya Wurno, Alhaji Abubakar Hamma’Ali da Alhaji Chika Hamma’Ali, na daga cikin manyan masu sauya sheka a karamar hukumar Wurno.

Alhaji Wurno, wanda yayi magana madadin masu sauya shekar, ya bayyana cewa sun koma APC ne saboda tarin nasarorin da Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ya samu lokacin da ya ke rike da mukamin gwamnan jihar.

Alhaji Mohammed Rabah, Alhaji Yusuf Mohammed Rabah, Alhaji Ango Shehu Rabah, da Alhaji Alhassan Ibrahim Rarah, na daga cikin anyan masu sauya sheka a karamar hukumar Rabah.

KU KARANTA KUMA: Dan takarar gwamna na APC a Kwara ya sha da kyar yayinda yan iska suka tarwatsa kamfen dinsa a Ilorin (hoto)

Sauran sune tsohon dan majalisar dokokin jihar Sokoto, Alhaji Ibrahim Tsamiya, wani tsohon mai ba gwamna Aminu Waziri Tambuwal shawara, Alhaji Husseini Gandi da kuma wani tsohon kansila, Alhaji Tukur Mohammed, da sauransu.

Shugaban APC a jihar, Aliyu Magatakarda Wamakko ya ba masu sauya shekar tabbacin cewa za a yi masu adalci kamar sauran tsoffin mambobin jam’iyyar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel