APC na fuskantar kalubale: Buhari bai damu da matasa ba - El-Bash

APC na fuskantar kalubale: Buhari bai damu da matasa ba - El-Bash

Anyi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, da ya waiwayi matasan da suka yi gwagwarmaya wajen kafuwar gwamnatinsa a 2015, da kuma ci gaba da kare muradun gwamnatin APC bayan samun nasarar zabe, wadanda ke kai gwauro da mari a kafafen sada zumunta na yanar gizo domin yada manufofin shugaban kasar.

Wani matashin dan siyasa, wanda kuma ya kware a wajen amfani da kafofin sada zumunta na yanar gizo, Bashir Abdullahi El-Bash, wanda yayi wannan kiran a zantawarsa da wakilin Legit.ng Hausa a Kano, ya kuma ce rashin nuna kulawar shugaban kasar ga wadannan matasa ya sanya suka fara dawowa daga rakiyarsa, inda tuni wasu suka fara komawa tafiyar Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP.

Bashir Abdullahi El-Bash, wanda makusanci ne ga mai tallafawa shugaban kasa Muhammadu Buhari ta fuskar kafofin sada zumunta, Bashir Ahmad, ya ce: "Akwai dumbin matasan da sun taimaka wajen kafuwar gwamnatin, kuma su na da shauki da zimmar tafiya karin karatu, amma gwamnatin ta gaza wajen yi musu wani tsari da zai taimaka musu wajen samun tallafin tafiya karatu."

KARANTA WANNAN: Duba matakan da zaka bi domin yin rejistar 2019 UTME - JAMB

Buhari ya yi watsi da matasa 'yan yanar gizo, suma sun fara watsi da shi - El- Bash

Buhari ya yi watsi da matasa 'yan yanar gizo, suma sun fara watsi da shi - El- Bash
Source: Twitter

  1. El-Bash, ya ce: "Kafin shugaba Muhammadu Buhari ya samu nasarar lashe zabe a (2015), ba za ka taba yarda ba idan wani ya rantse maka da Allah cewar matasan da su ke kwakwazo da kakatu a (New Media) kan baba Buhari za su zama abin wofintarwa a gwamnatin Buhari ba.

"Ba don komai ba, sai duba da yadda kowa ya gamsu dari-bisa-dari shugaba Buhari mutum ne mai son ganin al'umma musamman matasa sun ginu sun zauna da kafafuwansu kan dogaro da kai."

"Sai dai kash! Abin kunya abin takaici, yau ana daf da cinye shekaru hudu (4) na zangon farko na gwamnatin Buhari, har ma an fara shirye-shiryen tunkarar zabe a karo na biyu, amma babu wani matashi mai rajin kare muradu da manufofin gwamnatin Buhari a sabbin kafafen sadarwa na zamani (New Media), da za a daga a kalla a matsayin wanda gwamnatin Buhari ta yi wa silar zama wani abin alfahari kan dogaro da kai.

KARANTA WANNAN: Sanata Shehu Sani: Babu wani abun kirki da El-Rufai ya tsinanawa Kaduna

"Tabbas mun sani, ba mu jajirce wajen kafuwar wannan gwamnati domin ta wawuro mana dukiyar al'umma daga cikin baitulmali ta ba mu ba, duba da manufofinta na yaki da cin-hanci da rashawa, sai dai mun kyautata mata zaton za ta iya yi mana wani tsari na musamman da zai taimaka mana wajen kafuwa da duga-duganmu, ta yadda hakan zai kara taimaka mata wajen samar da ayyukan yi ga dumbin Matasan da ba sa aiki.

"Sanin kowa ne, akwai bambanci tsakanin hakkin dan 'yan 'kasa, da kuma hakkin wadanda su ka ba da gudunmawa wajen kafuwar gwamnati. Duk dan 'kasa ya na da hakki gwamnati ta kyautata masa ta kuma kula da damuwarsa, haka zalika, ba laifi ba ne ga duk wata gwamnati ta yi wani tsari na musamman da za ta taimakawa wadanda su ka taimaka ta kafu ba.

"Domin ko sarkin da ya yi mu, (Allah), tun a Duniya ya fifita wadan su ka taimaka wajen kafuwar addininsa a doron 'kasa fiye da wadanda ba su taimaka ba, kenan a babin Siyasa ma hakan ba laifi ba ne.

"Misali, Ni Bashir Abdullahi Elbash, ina da kamfani nawa na kaina da na ke gudanar da ayyukan yada labarai (Online), amma rashin gata da kulawar gwamnatin ya sanya har yau kamfanin ya kasa kaiwa ga cigaban da na ke da muradi duba da yadda harkar ta ke bukatar kayan aiki na zamani masu tsada. Da kuma ma'aikatan da zan na biya albashi, amma rashin kulawar gwamnatin ya sanya har yau cigaban kamfanin ya gaza kaiwa inda na ke da muradi balle na cigaba da taimakawa gwamnatin wajen rage mata marasa aiki a 'kasa, ta hanyar ba su aiki a kamfanina.

KARANTA WANNAN: Dalilin da yasa ya zama wajibi a jinjinawa shugaban kasa Buhari - Sanata Shehu Sani

Buhari ya yi watsi da matasa 'yan yanar gizo, suma sun fara watsi da shi - El- Bash

Buhari ya yi watsi da matasa 'yan yanar gizo, suma sun fara watsi da shi - El- Bash
Source: Facebook

"Haka zalika, akwai dumbin Matasan da sun taimaka wajen kafuwar gwamnatin, kuma su na da shauki da zimmar tafiya karin karatu, amma gwamnatin ta gaza wajen yi musu wani tsari da zai taimaka musu wajen samun tallafin tafiya karatu, duk kuwa da cewar gwamnatin ta na bayar da tallafin, amma ga matasan da su ka taimaka mata kuma sun cancanta amma an gaza shigar da su cikin tsarin.

"Haka zalika, wasu daga cikinmu 'yan kasuwa ne, tallafi su ke bukata na jari domin su samu nasarar bunkasa kasuwancisu har ma su iya samar da guraben aikin yi cikin al'ummominsu. Wasu kuma aikin gwamnati su ke bukata kuma sun cika duk wani sharada da ya kamata ace an ba su, amma duk gwamnatin ta yi ko'in kula akai.

"Kuma har yau an kasa samun gyara da kulawar da ta dace, tayadda har hakan ya fara fusata da dama daga cikinmu su ka fara yin hijira irin ta siyasa. Tayadda kuma hakan babban abin kunya ne da takaici, ace gwamnatin da su ka sadaukar akanta ta gaza share musu hawaye amma abokan adawa sun nemi su je gare su domin su share musu hawaye.

"Kuma har yanzu an gaza gane daga ina matsalar ta ke, wato ma'ana, shin baba Buhari ne ba ya son a taimakawa matasa, ko kuwa su mukarraban gwamnatin ne ba sa son a taimakawa matasan?, Hakika ya zama lallai a san a inda matsalar ta ke a kuma dau matakan gyara tun kafin sauran al'ummar gaba daya mu yi hijirar dole.

KARANTA WANNAN: Da dumi duminsa: Gwamnatin tarayya za ta ciyo bashin N823bn

"Domin matsalar ta yi kamarin da hatta gwamnatocin jihohi ba su damu da mutanen Baba Buhari ba masu ayyukan kare masa manufofi da muradu a (New Media) duba da yadda ba a sanya mu cikin duk wata harka ta cigaba a jihohinmu, sai dai a sanya iya masu kare muradun gwamna da mukarraban gwamnatin jiha.

"Hakika, mun sani cewa komawa gefe ba zai hana shugaba Muhammadu Buhari sake lashe zabe a karo na biyu ba, sai dai zai zama abin kunya ace yau matasan da su ka jima su na sadaukarwa akansa rashin kulawa da ake nuna musu a gwamnatinsa ya sanya sun yi kaura, kuma har sun samu gata da kykkyawar tarba a inda su ka je.

"Wannan abin kunya da zubar kimar Baba Buhari da gwamnatinsa a idon duniya, ba za mu so ace har ta kai ga hakan ba," a cewar El-Bash.

Daga karshe Bashir Abdullahi El-Bash ya baiwa masu ruwa da tsaki a gwamnatin shugaban kasa Buhari da APC, da su kira wadannan matasa masu yi mata aiki a kafafen sadarwa na zamani domin basu gudunmowa ta musamman da zata taimaka wajen bunkasa ayyukansu da tsayuwa da kafafunsu.

Ya ce hakan zai kara masu karfin gwiwar tunkarar zabe cikin karsashi da armashi har ma wasu mutanen masu adawa da gwamnatin su yi sha'awar kulawar da su ka ga an ba mu su ma su zo ayi tafiyar da su.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel