Murna a APC yayinda dan takarar gwamna na PDP ya sauya sheka a Jigawa

Murna a APC yayinda dan takarar gwamna na PDP ya sauya sheka a Jigawa

- Wani jigon PDP Alhaji Baba Aliyu Santali, ya sauya sheka zuwa jam’iyyar APC mai mulki

- Santali ya nemi takarar kujerar gwamnan jihar Jigawa a karkashin babbar jam’iyyar adawar kasar

- Yace ya yanke shawarar hakan ne sakamakon tarin nasarorin da gwamnatin APC ta samu a fadin kasar

Wani dan takarar kujerar gwamnan jihar Jigawa a karkashin jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP), Alhaji Baba Aliyu Santali, ya sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki.

Da yake kaddamar da hakan a bainar jama’a, Alhaji Baba Santali yace ya yanke shawarar hakan ne sakamakon tarin nasarorin da gwamnatin APC ta samu a fadin kasar.

Murna a APC yayinda dan takarar gwamna na PDP ya sauya sheka a Jigawa

Murna a APC yayinda dan takarar gwamna na PDP ya sauya sheka a Jigawa
Source: Depositphotos

Santali wanda ya kasance kwamishinan aiki da sufuri na tsawon shekaru takwas a karkashin tsohon Gwamna Sule Lamido, yayi bayanin cewa da gangan ya bari sai a karshen zangon APC na farko sannan ya bayyana kudirinsa saboda kore zargin da wasu za suyi kan cewa don a bashi mukami ne ya koma jam’iyyar.

KU KARANTA KUMA: Ta tabbata: Buhari da APC na son tarwatsa Nigeria - Uche Secondus

Santali yace ya dade yana goyo bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari tunda aka kafa kungiyar ‘The Buhari Organisation (TBO)‎.’

Santali ya sauya sheka ne tare da wasu shugabannin PDP daga mahaifar mataimakin shugaban PDP a yankin Arewa, Ambassador Ibrahim Kazaure.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel