Magoya Bayan APC Sama Da 500 Sun Sauya Sheka Zuwa PDP A Jihar Jigawa

Magoya Bayan APC Sama Da 500 Sun Sauya Sheka Zuwa PDP A Jihar Jigawa

Akalla mutane magoya bayan jam'iyyar All Progressive Congress (APC) 504 ne suka sauya sheka zuwa jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) a karamar hukumar Jahunb, jihar jigawa dake a shiyyar Arewa maso yammacin tarayyar Najeriya.

Yayin taron gangamin karbar 'yan siyasar, sun bayyana adalci da shugabanci abin misalin da Jagoran talakawa Dr. Sule Lamido CON, ya shuka a shekaru 8 da yayi a mulkinsa da cewar shine ya jawo hankalinsu zuwa jam'iyyar PDP.

Magoya Bayan APC Sama Da 500 Sun Sauya Sheka Zuwa PDP A Jihar Jigawa

Magoya Bayan APC Sama Da 500 Sun Sauya Sheka Zuwa PDP A Jihar Jigawa
Source: UGC

KU KARANTA: "Buhari ya tsiyatar da Dangote"

Suka kara da cewa daman Sule Lamido ne ya samar masu da hanyar da suka yi shekara da shekaru suna nema, wadda suka ce da jamiyyar PDP ce take mulki da tuni an mayar da hanyar zuwa kwalta lena.

Haka zalika kuma sun bayyana aniyarsu da cewar zasu bayar da dukkan gudunmawarsu domin tabbatar da nasarar jam'iyyar PDP.

Sun bayyana k'arya, yaudara da APC tayi musu da cewar abin kaico ne da Allah wadarai sun yi mulki shekaru 4 babu abinda suka yi musu sai alk'awari da ba'a cikawa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel