Mutane 2 sun yi asarar rayuwarsu a rikicin kabilanci daya barke a Kogi

Mutane 2 sun yi asarar rayuwarsu a rikicin kabilanci daya barke a Kogi

Rundunar Yansandan jahar Kogi ta tabbatar da mutuwar mutane biyu a sanadiyyar wata tsohuwar gaba da aka tayar dake tsakanin wasu kabilu biyu da suka hada da kabilar Ibira da kabilar Bassa-Kwomu, inji rahoton kamfanin dillancin labaru, NAN.

Majiyar Legit.com ta ruwaito kaakakin rundunar, DSP William Aya ne ya tabbatar da aukuwar lamarin a garin Lokoja, inda yace rikicin ya faru ne a daidai lokacin da wasu jama’an kabilar Ibira suka koma garin Oguma, babban garin karamar hukumar Bassa.

KU KARANTA; Atiku ya zargi Buhari da APC sun kwashe kudin gwamnati suna yakin neman zabe dasu

Mutane 2 sun yi asarar rayuwarsu a rikicin kabilanci daya barke a Kogi

Wani Rikici
Source: UGC

Rahotanni sun tabbatar da cewar jama’an Ibira su fice daga garin ne sakamakon wani rikici da aka taba yi a baya tsakaninsu da jama’an kabilar Bassa-Kwomu, sai dai daga bisani sun matsa akan sai sun koma bayan kura ta lada, tunda a cewarsu garinsu ne, kuma garin iyaye da kakanni.

Kaakakin Yansanda yace a ranar da zasu koma garin Oguma, gwamnati ta hadasu da jami’an tsaro da dama da kuma shuwagabannin siyasa daga ciki har da shugaban karamar hukumar Bassa, Samuel Alumka domin su rakasu zuwa garin nasu.

Fatan gwamatin jahar Kogi shine ganin tawagar jami’an tsaro data manyan mutanen data sanya su raka yan kabilar Ibira zuwa garin Oguma zai kwantar da hankulansu, tare da karesu daga duk wani hari da yan kabilar Bassa Kwomu zasu kai musu.

Sai dai da ayarin ta isa fadar Sarkin Bassa-Kwomu, Aguma Bassa, Cif William Keke, sai manyan garin suka sanya baki cikin lamarin, amma a maimakon su kashe wutar, sai suka sake rurata, inda suka ce kada wani Ibira ya sake taka kafa a garinsu, su koma inda suka fito.

Wannan batu na Aguma Bassa da manyan fadarsa ne ya harzuka yan kabilar Ibira, inda nan take wani sabon rikici ya sake kaurewa a tsakaninsu da yan kabiya Bassa-Kwomu, inda aka kashe mutane biyu tare da jikkata wasu da dama.

Sai dai kaakakin yansandan jahar Kogi yace jami’ansu sun samu nasarar shawo kan matsalar tare da kwantar da tarzomar, inda yace a yanzu haka sun baza manya da kananan Yansanda da kuma Sojoji daga rundunar Sojan kasa don kwantar da hankula.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel