Shugaba Buhari ba wani mai gaskiya bane da mutane ke tunani can-can - Saraki

Shugaba Buhari ba wani mai gaskiya bane da mutane ke tunani can-can - Saraki

Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, ya bayyana cewa Shugaba Muhammadu Buhari ba fa mutum nagari mai gaskiya ba ne kamar yadda ake ta kururuwa a kan sa.

Saraki ya ce gwamnatin Buhari gwamnati ce ta mahandama da kuma wawurar kudaden jama’a.

Legit.ng Hausa ta samu cewa da ya ke jawabi a Gidan Talbijin na Channels, a matsayin Saraki na Darakta Janar na Kamfen din Atiku, ya ce Buhari ya rungumi masu kashi a gindi ya goya, don haka kimar sa da kallon da ake yi masa na mai gaskiya, ta zube a kasa warwas.

Shugaba Buhari ba wani mai gaskiya bane da mutane ke tunani can-can - Saraki

Shugaba Buhari ba wani mai gaskiya bane da mutane ke tunani can-can - Saraki
Source: UGC

KU KARANTA: Hajara Usman ma ta bayyana wanda za ta zaba a 2019

“Ko shakka babu akwai marasa gaskiya a kewaye da Buhari. Idan da gaske Buhari ya na yaki da cin rashawa ne, ina mamakin yadda har yau an ki hukunta wadanda ake zargi da ke kewaye da shi.”

“Matsawar ka na shugaba, amma ka ki bari a hukunta wadanda ke kewaye da kai, to wace nagarta kuma za a sake kallon ka na da ita?”

Da aka tambaye shi ko shi Buhari din ya na cuwa-cuwa? Sai ya ce gwamnatin sa gwamnatin cuwa-cuwa ce don haka idan ana yi ba ka hukunta masu yi, ai kamar ka amince ne, ko ka bayar da kofa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel