Sai da ya kashe 'yan Boko Haram 15 kafin suka kashe shi - Labarin wani soja

Sai da ya kashe 'yan Boko Haram 15 kafin suka kashe shi - Labarin wani soja

Za a iya cewa ta'addancin mayakan Boko Haram na ci gaba da daukar sabon salo, musamman yawaitar hare haren da suke kaiwan dakarun sojin Nigeria a baya bayan nan, sai dai har yanzu labarin mutuwar dakarun sojin ya gaza samun wani tagomashi, musamman yadda ake boye labaran bajintar da suka yi kafin mutuwar tasu.

Kamar yadda shafin Legit.ng Hausa ya samu rahoto daga jaridar Saharareporters, dangane da mamayar da Boko Haram ta kai sansanin soji na Monguno, jihar Borno, a karshen makon 2018, sojan da aka kashe, ya rasa ransa ne a wajen bajinta, wanda bai mutu ba sai da ya kashe sama da mayakan Boko Haram din 14.

"Muna zazzaune a lokacin da mayakan Boko Haram suka kawo mana wannan farmaki," cewar wani soja da ya tsallake rijiya ta baya baya a lokacin da 'yan ta'addan suka kai harin, kamar yadda ya labartawa SaharaReporters yadda komai ya faru, a ranar Alhamis.

"Abu na farko da muka fara yi shine tserewa don neman mafaka. Munyi gudu har sai da muka riski wani waje da aka killace shi da wayoyi masu tsini. Wajen na kulle."

KARANTA WANNAN: Duba matakan da zaka bi domin yin rejistar 2019 UTME - JAMB

Sai da ya kashe 'yan Boko Haram 15 kafin suka kashe shi - Labarin wani soja
Sai da ya kashe 'yan Boko Haram 15 kafin suka kashe shi - Labarin wani soja
Asali: UGC

Direban da ke tuka motar ya sauka tare da harbin kwadon wajen da bindiga, inda muka samu hanyar kutsawa ciki, a nan ma muka ci gaba da gudu, muka samu wani babban rami, watakil nan ne mabuyar 'yan ta'addan. Da muka bincika muka hakikance akwai 'yan ta'addan a ciki.

"Ganin hakan ne ya sa shi direban namu, ya sauko daga motar, ya karbi bindigarsa, ya kutsa kai a cikin ramin inda ya ci gaba da barin wuta akan mayakan na Boko Haram.

"Ya kashe sama da mayakan Boko Haram 14 kafin suka kashe shi. Yana kashe su yana kara kutsawa cikinsu. Sai dai akwai wani dan ta'adda da ya harba, ya dauka ya mutu; wannan dan ta'addan ne ya samu karfin da ya harbe shi ta baya, idan ba domin hakan ba, da ya kashe su da dama. Tuni dama ya kashe su da yawa, sama da mutane 14."

Soja daya ne daga cikinsu, wannan direban, ya mutu a wannan harin, yayin da sauran suka samu raunuka kawai. Amma a wani hari da ya faru a wannan makon da 'yan ta'addan suka kwace garin Baga, an kashe sojoji da dama, yayin da aka nemi sama da 700 aka rasa, labarin ya zama abun rikitarwa.

"Babu wanda ya tsaya don ya yake su. Kowa guduwa yake yi, saboda Boko Haram ta zo da manyan makamai na ban mamaki. Duk wasu labarai da rundunar soji ke cewa dangane da sayawa sojoji makamai, duk karya ce. Bamu da makaman da Boko Haram ke da su," a cewar sojan.

"Ba zaka taba hada kanka da ke rike da wuka wai kace kana kokarin yakar wanda ke rike da adda mai kaifi ba. Ka duba wannan misalin fa, wukarka bata da tsawo, kuma bata da kaifi. Amma shi, abokin hamayyarka yana rike da doguwar adda. Tabbas shine zai samu nasara akanka.

"Don haka, wannan ce matsalar da muke fuskanta; rashin makamai. Ku kalli Baga, Boko Haram ta kwaceta daga hannun soji. Abun takaicin shine akwai wani dakin ajiye masu laifi a sansanin rundunar sojin inda ake kulle sojoji da mayakan Boko Haram. A lokacin da Boko Haram ta fatattaki kowa, sun bude daki. Me kake tunanin zai faru da sojojin da ke cikin wannan dakin? Babu makawa, kashe su zasu yi."

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel