Sarkin Lafia Isa Mustapha Agwai ya rasu yana da shekaru 84

Sarkin Lafia Isa Mustapha Agwai ya rasu yana da shekaru 84

Alhaji Isa Mustapha Agwai I, sarkin Lafia kuma shugaban kungiyar sarakunan jihar Nasarawa ya mutu yana da shekaru 84 a duniya.

Alhaji Sule Abubakar, Ajiyan-Lafiya ya tabbatar da mutuwar babban sarkin ga manema labarai a ranar Alhamis, 10 ga watan Janairu, a Lafia, kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ta ruwaito.

A cewar babban jami’i a masarautar, sarkin ya rasu ne a ranar Alhamis, 10 ga watan Janairu, a asibitin koyarwa na Turkiya da ke Abuja bayan fama da rashin lafiya.

Sarkin Lafia Isa Mustapha Agwai ya rasu yana da shekaru 84

Sarkin Lafia Isa Mustapha Agwai ya rasu yana da shekaru 84
Source: UGC

Yace an nada ma sarkin sarauta a ranar 28 ga watan Mayu, 1974, sannan kuma kwanakin baya yayi bikin cika shekaru 44 akan mulki.

Marigayin sarkin ya mutu ya bar mata uku da yara biyu.

KU KARANTA KUMA: Kada ku zabi barayin shugabanni, ku zabi Buhari – Adamu

A wani rahoto na daba, sarkin Nasarawa, Alhaji Ibrahim Usmna Jibrin, yayi kira ga yan siyasa da suyi siyasa da tsoron Allah.

Daily Trust ta ruwaito cewa yayi kiran ne a fadarsa a karshen mako yayinda ya karbi bakoncin dan takarar kujerar sanata na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a yankin Nasarawa ta yamma, Sanata Abdullahi Adamu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel