Kannywood: Fim din Yaki A Soyayya ya shiga sahun manyan fina-finar 20 a Najeriya

Kannywood: Fim din Yaki A Soyayya ya shiga sahun manyan fina-finar 20 a Najeriya

- Fim din Kannywood mai suna ‘Yaki A Soyayya’ ya shiga rukunin mayan fina-finan Najeriya 20

- Yaki A Soyayya shine na 17 cikin fia-finai 20 da aka haska a sinima a fadin kasar daga ranar 28 ga watan Disamban 2018 zuwa ranar 3 ga watan Janairun 2019

- Furodusar fim din Nafisa Abdullahi tace tayi matukar farin ciki da fim dinta ya shiga jerin manyan fina-finai 20 a fadin Najeriya baki daya

Shahararren fim dinnan na Kannywood mai suna ‘Yaki A Soyayya’ ya shiga rukunin mayan fina-finan Najeriya 20.

Fim din ‘Yaki A Soyayya’ shine na 17 cikin fina-finai 20 da aka haska a sinima a fadin kasar daga ranar 28 ga watan Disamban 2018 zuwa ranar 3 ga watan Janairun 2019.

Kannywood: Fim din Yaki A Soyayya ya shiga sahun manyan fina-finar 20 a Najeriya
Kannywood: Fim din Yaki A Soyayya ya shiga sahun manyan fina-finar 20 a Najeriya
Asali: UGC

Kungiyar sinima na Najeriya wato Cinema Exhibitors Association of Nigeria (CEAN) ce ta saki jerin fina-finan a shafinta na twitter a ranar Laraba, 9 ga watan Janairu.

KU KARANTA KUMA: Nyako ya roki mutanen Adamawa da su zabi dan sa na jam’iyyar ADC a matsayin gwamnan jihar

Kungiyar tayi bayanin cewa jerin fina-finan na daidai da bayanan yadda fina-finan suka yi fice a kullun a sinimomin Najeriya.

Daga jerin fina-finan, Yaki A Soyayya ta samu N722,000 a karshen mako sannan kimanin N1, 276, 000 a cikin kwanaki 7 kacal.

Da take martani, wacce ta shirya fim din Yaki A Soyayya, Nafisa Abdullahi tace tayi matukar farin ciki da fim dinta ya shiga jerin manyan fina-finai 20 a fadin Najeriya baki daya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel