Nyako ya roki mutanen Adamawa da su zabi dan sa na jam’iyyar ADC a matsayin gwamnan jihar

Nyako ya roki mutanen Adamawa da su zabi dan sa na jam’iyyar ADC a matsayin gwamnan jihar

- Murtala Nyako ya roki jama'an jihar da su yi masa kara su zabi dansa AbdulAzeez Nyako da ke takarar kujerar gwamnan jihar

- Yace dan nasa ne zai dawo da martabar jihar da gwamna mai ci Jibirilla Bindow ya yagalgala a idanun mutane

Tsohon gwamnan jihar Adamawa Murtala Nyako ya roki al’umman jihar da su yi masa kara su zabi dansa AbdulAzeez Nyako da ke takarar kujerar gwamnan jihar a karkashin inuwar jam’iyyar ADC a matsayin gwamnan jihar.

A cewar Nyako dan nasa ne zai dawo da martabar jihar da gwamna mai ci Jibirilla Bindow ya yagalgala a idanun mutane.

Nyako ya roki mutanen Adamawa da su zabi dan sa na jam’iyyar ADC a matsayin gwamnan jihar
Nyako ya roki mutanen Adamawa da su zabi dan sa na jam’iyyar ADC a matsayin gwamnan jihar
Asali: Facebook

Yace: “Lokaci yayi da mutanen jihar za su dawo daga rakiyar gwamna mai ci wato Jibirilla Bindow, jama’a su canja shi da dana na jam’iyyar ADC. A gwada jam’iyyar ADC.

“Bindow da jam’iyyar sa ta APC sun ba mutanen Adamawa kunya matuka domin kuwa babu wani abin azo a gani da gwamnatin ta tabuka a shekarun da tayi ta na mulki a jihar.”

KU KARANTA KUMA: PDP ta rasa mambobinta 450 a Akwa Ibom

A wani lamari na daban, mun samu labari daga Jaridar The Cable cewa Kingsley Mogahalu wanda yana cikin masu harin kujerar shugaban kasa a zaben bana na 2019 ya kashe akalla Naira Miliyan 200 kawo yanzu wajen neman takara.

Kingsley Moghalu, wanda ya fito takarar shugaban kasa a jam’iyyar adawa ta YPP yace ya batar da abin da ya haura Naira miliyan 200 daga aljihun sa. Moghalu ya bayyyana wannan ne lokacin da ya zauna da jama’a a wata hira da NTA jiya.

‘Dan takarar ya bayyana cewa bai da wani uban gida da ya tsaya masa, don haka da kudin sa yake amfani wajen neman takarar shugaban kasa, sannan kuma ya bayyana cewa zai samu sauran kudin kamfe ne daga masu bada gudumuwa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Leit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel