Dandalin Kannywood: Hajara Usman ta fadi wa zata zaba a matsayin shugaban kasa a 2019

Dandalin Kannywood: Hajara Usman ta fadi wa zata zaba a matsayin shugaban kasa a 2019

Fitacciyyar jaruma kuma daya daga cikin iyaye a masana'antar shirya fina-finan Hausa da aka fi sani da Kannywood watau Hajara Usman ta bayyana wanda zata goyawa baya a zaben gama gari na shekarar nan ta 2019 a matsayin shugaban kasa.

Jarumar dai ta bayyana cewa in Allah ya yarda zata yi aiki tare domin samun nasarar Shugaba Muhammadu Buhari a zabe mai zuwa kamar da yawa daga cikin jaruman masana'antar.

Dandalin Kannywood: Hajara Usman ta fadi wa zata zaba a matsayin shugaban kasa a 2019

Dandalin Kannywood: Hajara Usman ta fadi wa zata zaba a matsayin shugaban kasa a 2019
Source: Facebook

KU KARANTA: Buhari ya amince a kafa sabbin jami'o'i 4 a Najeriya

"Ba zai yiwu a ce dukkaninmu, kowa da kowa sunansa yana cikin jadawalin sunayen masu gudanar da yakin neman zaben jam'iyyar APC ba.

"Amma in sha Allahu dukkaninmu za mu yi aiki tare domin samun nasarar Shugaba Muhammadu Buhari a zabe mai zuwa, kuma a tare za mu yi bikin samun nasara idan Allah ya yarda", tace.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa a kwanan baya ne dai shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gayyaci wasu daga cikin jaruman Kannywood ciki hadda ita Hajara Usman din a fadar sa inda ya jinjina masu kan goyon bayan da suke nuna masa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel