Gwamnatin Jihar Neja Ta Rufe Babban Gidan Shaye Shaye Da Badala A Kontagora
A cigaba da kokarin kawar da aiyukan badala a fadin Jihar, gwamnatin Jihar Neja ta tura tawaga na musamman karkashin jagorancin CSP Muhammad Umar Dakingari da suka hada da sauran jami'an tsaron dake a jihar zuwa garin Kwantagora domin tsaftace jihar da tabbatar da da'a.
Jami'an da aka tura dai sun hada da 'yan sanda, sojoji, NDLEA, HISBA da sauran su kuma sun je ne domin surufe shahararrun gidajen saida kayan barasa da aikata miyagun aiyukan da suka hada da zinace, zinace dake Kontagora.

Asali: Twitter
KU KARANTA: Taron PDP a jihar Jigawa ya tashi ba shiri
Legit.ng Hausa ta samu cewa cikin gidajen da aka rufe hadda shahararren wurin nan wanda yayi kaurin suna wajen tafka ayyukan assha akafi sani da "Bush Bar" dake wuraren barikin sojoji na Nagwamatse Barack Kontagora.
Shugaban sashen kawar da haramtattun gidajen giya na hukumar LIQUORE ta Jihar Neja Malam Usman Lapai ya baiyana cewar sun dauki matakin rufe wannan wuri ne sakamakon rahoton munanan aiyukan da ake aikatawa a wurin wanda kwata kwata ya sabawa dokokin Jihar.
Wannan wuri dai yayi kaurin suna wurin zama matattaran aikata aiyukan assha, da suka hada da shaye shaye, raye raye na mata da maza tsirara, madigo da luwadi, lalata tarbiyyar kananan yara maza da mata wanda hakan ke ciwa dukkan wani dan Kontagora mai kishi tuwo a kwarya.
Ga dai wasu hotunan nan na karuwan:

Asali: Facebook

Asali: Facebook

Asali: Facebook
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng