Lissafi: Jihohi uku da duk wanda ya lashe kuri’unsu, ya lashe zaben 2019

Lissafi: Jihohi uku da duk wanda ya lashe kuri’unsu, ya lashe zaben 2019

A ranar Litinin din da ta gabata ne hukumar zabe ta kasa watau INEC, ta gabatar da jimilla ta adadin al'ummar kasar nan da suka shiryawa babban zabe na 2019. Hukumar ta ce 'yan Najeriya 84,004,084 ke da rajista ta cancantar kada kuri'u a zaben.

Yayin gabatar da wannan adadi a gaban shugabannin jam'iyyun kasar nan, shugaban hukumar zabe, Farfesa Mahmoud Yakubu, ya ce jihar Legas da kuma Kano sun sake kasancewa kan gaba wajen yawan adadin masu zabe a bana.

A lissafin da Legit.ng tayi, duk dan takaran da ya lashe kuri’un jihohi uku mafi yawan masu zabe a kasa ne ake kyautata zaton ya zai lashe zaben.

KU KARANTA:Yan takaran gwamna 11 sun koma jam'iyyar APC

Ga jihohin da dalilanmu:

1. Jihar Legas: Wannan jihar ce mafi yawan mutane da ke rike katin zabensu kuma ana sa ran zasu kada kuri’a a watan gobe. Bisa ga adadin da hukumar INEC ta saki, jihar Legas na da jama’a masu zabe milyan shida, dubu dari biyar da saba’in, da dari biyu da tis’in da daya (6.570,291).

Wannan na nuna cewa kuri’un mutan jihar Legas kadai yafi na jimillan jihohin Bayelsa, Ekiti, Gombe, Sokoto da Abuja. Adadin masu kada kuri’ar jihohin nan gaba daya 6,476,164 ne.

2. Jihar Kano: Kanon dabo ce jiha ta biyu a jerin jihohi mafi yawan kuri’u zaben bana da za’a gudanar, Bisa ga adadin da hukumar INEC ta saki, jihar Kano na da masu zabe liyan biyar,dubu dari hudu da hamsin da bakwai, dari bakwai da arbain da bakwai ( 5,457,747).

Wannan na nuna cewa kuri’un mutan jihar Kano kadai yafi yawan jimillan kuri’un mutanen jihohi Yobe, Gombe da Plateau a hade.

3. Jihar Kaduna: Kaduna wacce akafi sani da garin gwamna ce jiha ta uku mafi yawan masu zabe a 2019. INEC ta bayyana cewa adadin mutanen da ke rike da katin zabensu a yanzu shine milyan uku, dubu dari tara da talatin da biyu, dari hudu da tis’in da biyu ( 3,932,492). Idan ka hada yawan masu zabe jihar Ebonyi da Kwara, da kuma rabin na jihar, ba kai yawan kuri’un mutan jihar Kaduna ba.

A karshe, lissafinmu ya nuna cewa duk dan takaran shugaban kasan da ya lashe zaben jihar Kano, Legas da Kaduna, kamar ya lashe zabe jihohi goma ne kamar Bayelsa,Ektii, Gombe, Sokoto, Abuja, Yobe, Gombe, Plateau, Kwara, Ebonyi da Edo.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel