Watsa min acid ya kara min kwarin gwiwa ne – Nura M Inuwa

Watsa min acid ya kara min kwarin gwiwa ne – Nura M Inuwa

Shahararren mawakin fina-finan Hausa nan, Nura M Inuwa, ya bayyana yadda ya samu kwarin gwiwa bayan da aka watsa masa acid.

Mawakin ya bayyana hakan ne a wata hira na musamman da ya yi da BBC a kwanakin baya.

Nura ya ce abin da ya same shin ya kara masa son jama'a ne, maimakon gudun su.

Ga yadda cikakken hirar ta kaya da shi. “Ina yaro na fara da kuruciya, kawai sai na tsinci kaina ina waka a baya.Idan an bata min rai na kan yi waka, idan an faranta min rai hakan, na kan yi waka.”

Da aka tambaye shi akan mai ya dauki matsayin waka, Nura yace “Na dauke ta a matsayin sana’a.

“Tana yi man amfani wajen tura sakonnin gyara ga al’umma. Fadakarwa da kuma nishadantarwa."

Watsa min acid ya kara min kwarin gwiwa ne – Nura M Inuwa
Watsa min acid ya kara min kwarin gwiwa ne – Nura M Inuwa
Source: UGC

Mu’azzam Idi Yari ne ya fara daura Nura M Inuwa akan hanyar waka.

“Sai ya rubuta wakar ya bani, salon kida, toh bayan ya bani nima da na karbe ta sai naje na ciccire wasu maganganu da nake ganin sun yi mani tsufa a cikin wakar, na gyara ta, nayi ta, ita ce wakar Salon Kida.

“Na yarda Allah zai yi mun, kuma yayi mun. Shi ya cusa wa mutane kaunar wakokina a zukatansu suke son jin wakokina."

Da aka tambaye shi kan yaushe aka watsa mai guba yace: “A ranar Asabar ne kuma suka ce suna so su zo su koma Abuja, kuma shi wanda ya kira ni cewa matarsa, wadda zai aura c eta dage sai Nura M Inuwa ya yi mata waka.

“Ni kuma kusan duk lokacin da aka yi mani irin wannan maganganun sai a karya mani zuciyata. Wannan dalilin yasa suka kira ni, suka yaudare ni da sana’ata. Suka watsa min acid.

“Wannan ya zama kusan tambari ko shaidar Nura M Inuwa nan, idan ka gan shi said a gilas, idan babu gilas, ton bashi bane.”

KU KARANTA KUMA: Uwargidan gwamna Bagudu ta fara yiwa Buhari kamfen din gida-gida a Kebbi

An tambaye shi kan mehakan ya janyo wajen koma baya ko ci gaban rayuwarsa sai yace: “Na samu kwarin gwiwar abunda nake yi, sannan ya sa mun kaunar mutane. Idan da yayi tasirin da zai sa ni in dunga gudun mutane nan ma da ya zama matsala gareni, tunda zan samu raguwar masoyana, saboda zan ce ban yarda da kowa ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel