2019: Yawan adadin masu rajistan zabe na kowace Jiha

2019: Yawan adadin masu rajistan zabe na kowace Jiha

Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta ta fitar da bayanai akan yawan yan takarar da ta yi wa rijista sannan ake sanya ran za su kada kuri’u a zabe mai zuwa. Bayanan ya nuna cewa yankin Arewa Maso Yamma ne ta fi ko wacce yanki yawan masu rijistan zabe a 2019.

Akwai masu rijistar zabe har miliyan 20 daga yankin Arewa Maso gabas, Kudu Maso Yamma na da mutanen da suka yi rijista miliyan 16.

Yankin Kudu Maso Kudu na da miliyan 12, Kudu Maso Gabas Miliyan 10, Arewa Maso Gabas Miliyan 11 sannan Arewa ta Tsakiya Miliyan 13.

Matasa ‘yan shekara 18 – 35 ne suka fi yawan masu kada kuri’a da kashi 51.11 bisa 100 na masu zabe.

KU KARANTA KUMA: Ka ajiye kudi akan tebur tare da Buhari a daki, za ka ga kudinka idan ka dawo - Tinubu

36 – 50 kuma kashi 29.9 bisa 100, 51 – 70 kashi 15.2 sannan kuma daga 70 zuwa sama, kashi 3.6.

Ga cikakken bayani game da yawan adadin masu rijista ta kowace jiha a kasa:

1. Jihar Abia 1,932,892

2. Jihar Adamawa 1,973,083

3. Jihar Akwa Ibom 2,119,727

4. Jihar Anambra 2,447,996

5. Jihar Bauchi 2,462,843

6. Jihar Bayelsa 923,182

7. Jihar Benue 2,480,131

8. Jihar Borno 2,315,956

9. Jihar Cross River 1,527,289

10. Jihar Delta 2,845,274

11. Jihar Ebonyi 1,459,933

12. Jihar Edo 2,210,534

13. Jihar Ekiti 909,967

14. Jihar Enugu 1,944,016

15. Babbar birnin tarayya Abuja 1,344,856

16. Jihar Gombe 1,394,393

17. Jihar Imo 2,272,293

18. Jihar Jigawa 2,111,106

19. Jihar Kaduna 3,932,492

20. Jihar Kano 5,457,747

21.Jihar Katsina 3,230,230

22. Jihar Kogi 1,646,350bi 1,806,231

23. Jihar Kogi 1,646,350

24. Jihar Kwara 1,406,457

25. Jihar Lagos 6.570,291

26. Jihar Nasarawa 1,617,786

27. Jihar Niger 2,390,035

28. Jihar Ogun-2,375,003

29. Jihar Ondo-1,822,346

30. Jihar Osun 1,680,498

31. Jihar Oyo 2,934,107

32. Jihar Plateau 2,480,455

33. Jihar Rivers 3,215,273

34. Jihar Sokoto 1,903,166

35. Jihar Taraba 1,777,105

36. Jihar Yobe 1,365,913

37. Jihar Zamfara 1,717,128

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel