Yanzu-yanzu: Gwamnatin tarayya ta yi gabatar da muradun mafi karancin albashin N30,000 gaban majalisa ranan 23 ga wata

Yanzu-yanzu: Gwamnatin tarayya ta yi gabatar da muradun mafi karancin albashin N30,000 gaban majalisa ranan 23 ga wata

Labarin da ke shigo mana da dumi-dumi na nuna cewa gwamnatin tarayya ta yi alkawarin gabatar da takardar dokan mafi karancin albashin N30,000 gaban majalisar dokokin tarayya ranan 23 ga wata domin tabbatar da shi.

Ministan kwadago da samar da aikin yi, Dakta Chris Ngige, ya bayyana hakan ne a ranan Talata, 8 ga watan Junairu, 8 ga watan Junairu 2018 a ganawar da wakilan gwamnatin tayi a yan kungiyar kwadago a birnin tarayya Abuja.

Wakilan gwamnatin tarayya da na kungiyar kwadago NLC sun dade suna ganawa daban-daban kan yadda za'a samar da sabuwar dokar mafi karancin albashi domin kawar da yajin aikin da ma'aikata sukayi barazanar zasuyi.

KU KARANTA: Mazauna kauyen Pakudi sun tsere daga muhallansu bayan wani manomi ya kashe makiyayi

Mun kawo muku rahoton cewa kungiyar kwadago NLC reshen jihar Cross River, ta ce ba zata shiga cikin zaben 2019 ba, ma damar gwamnatin tarayya ta gaza kaddamar da N30,000 a matsayin mafi karancin albashi ga ma'aikatan kasar.

Shugaban kungiyar NLC na jihar, Mr John Ushie, ya bayyana hakan a ranar Talata a yayin da mambobin kungiyar suka gudanar da zanga zangar lumana don ganin cewa gwamnatin tarayyar ta kaddamar da wannan albashi mafi karanci.

Ushie ya ce albashi mafi karanci na ma'aikatan a yanzu, N18,000 ya kamata ya canja tun 2015, kuma ya zargi gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari da yin wasa da hankalin ma'aikatan kasar ta hanyar daukar alkawurra da dama ba tare da cikawa ba.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com\

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel