Asiri ya tonu: Yadda aka shirya kashe Atiku, Saraki a wajen yakin zabe

Asiri ya tonu: Yadda aka shirya kashe Atiku, Saraki a wajen yakin zabe

- Comrade Time Frank ya ce sun bankado wani shiri na kashe Alhaji Atiku Abubakar da, Sanata Abubakar Bukola Saraki, a wajen yakin zabe, a wata jihar Arewa

- Haka zalika, Frank ya ce idan har wani abu ya samu Atiku da Saraki a wajen wani yakin zabe, to kuwa gwamnatin APC ce zata dauki alhakin hakan

- Dan siyasar ya kuma yi tuni da yadda matar Atiku da yaronsa suka tsallake rijiya ta baya baya, da kuma irin sakwannin barazana da suke samu a wayoyinsu a 2018

Tsohon mataimakin sakataren watsa labarai na jam'iyyar APC na kasa, Comrade Time Frank ya ce sun bankado wani shiri na kashe dan takarar shugaban kasa karkashin PDP, Alhaji Atiku Abubakar da daraktan yakin zabensa, Sanata Abubakar Bukola Saraki, a wajen yakin zabe, a wata jihar Arewa.

Haka zalika, Frank ya aike da waska ga kasashen ketare akan su ja kunnen shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da umurtarshi da kuma sanar da duniya cewa idan har wani abu ya samu Atiku da Saraki ko wani shugaban PDP a wajen wani yakin zabe, to kuwa gwamnatin APC ce zata dauki alhakin hakan.

Wasikar wacce ya kuma aikewa Majalisar Dinkin Duniya, kungiyar hadakar kasashen Afrika AU, gwamnatin Amurka, gwamnatin kasar Burtaniya da Canada da dai sauransu, ta sanar da kasashen duniyar cewa akwai cin mutunci da hukunta jiga jigan abokan hamayya da gwamnatin Buhari take yi da sunan yaki da cin hanci da rashawa.

KARANTA WANNAN: Gwamna Masari: Katsina zata dauki matakan da suka dace na kawo karshen ta'addanci

Asiri ya tonu: Yadda aka shirya kashe Atiku, Saraki a wajen yakin zabe
Asiri ya tonu: Yadda aka shirya kashe Atiku, Saraki a wajen yakin zabe
Asali: Facebook

Da yake yin wannan zargi a ranar Talata cikin wata sanarwa a Abuja, Timi Frank ya ce bayanan da suka samu daga majiya mai tushe a cikin jami'an tsaro, na nuni da cewa gwamnati mai c a yanzu na yunkurin amfani da 'yan ta'adda wajen haddasa rikici a wani taron yakin zaben PDP musamman a wata jihar Arewa, inda a nan ne jami'in dan sanda zai harbi DG (Saraki) ko Alhaji Atiku, wanda za a alakanta kisan da yunkurin dakile 'yan bangar siyasar.

Frank ya ce tun farko an shirya aiwatar da kisan ne a yakin zaben PDP na jihar Kogi da ya gudana a ranar Litinin, amma shuwagabannin PDP na jihar suka samu abarin shirin tare da daukar matakin gaggawa.

Idan za a iya tunawa a cikin wata sanarwa daga shugaban sashen watsa labarai na kungiyar yakin zaben Atiku, Usman Austin Okai, PDP ta yi zargin cewa akwai yunkurin da ake yi na kashe dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP da iyalansa.

A cewar Timi Frank, hanya daya da gwamnati mai ci a yanzu zata iya dakie Atiku Abubakar daga zama shugaban kasar na gaba shine ta hanyar kulla makircin kashe shi, kamar yadda tuni gwamnatin Buhari ta kulla yin hakan.

Dan siyasar ya kuma yi tuni da yadda matar Atiku Abubakar da yaronsa suka tsallake rijiya ta baya baya, da kuma irin sakwannin barazana da suke samu a wayoyinsu a shekarar 2018, duk da cewa na aikewa shugaban kasa Buhari wasika kan hakan, babu wani mataki da gwamnatin ta dauka.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel