Ranar zabe: Kiristocin jihar Kano sun bayyana wanda za su zaba a zaben 2019

Ranar zabe: Kiristocin jihar Kano sun bayyana wanda za su zaba a zaben 2019

A karshen makon da ya gabata ne dai maibawa shugaban kasa shawara harkar majalisa Honarabul Kawu Sumaila ya karbi bakuncin wasu 'yan kungiyar kiristoci na kudancin Kano wadanda suka ce ba su da dan takarar shugaban kasa a zaben 2019 face Muhammad Buhari.

Su dai kiristocin sun babbana haka ne jim kadan bayan sun kammala wata muhimmiyyar tattaunawa da maibawa shugaban kasa shawara harkar majalisa Honarabul Kawu Sumaila a jihar ta Kano.

Ranar zabe: Kiristocin jihar Kano sun bayyana wanda za su zaba a zaben 2019

Ranar zabe: Kiristocin jihar Kano sun bayyana wanda za su zaba a zaben 2019
Source: UGC

KU KARANTA: An cimma yarjejeniya tsakanin ASUU da gwamnatin tarayya

Legit.ng Hausa ta samu cewa dai zaben na 2019 ana sa ran zai shiga tarihi a matsayin zabe mafi zafi a tarayyar Najeriya saboda yanayin karfin dukkan 'yar takarkarin da kuma kasancewar su 'yan addini da kuma kabila daya.

A wani labarin kuma, Gwamnatin tarayyar Najeriya tace ta cimma yarjejeniya tsakanin ta da kungiyar malaman jami'o'in karar nan watau Academic Staff Union of Universities (ASUU) a turance da yanzu haka ke yajin aiki tun watan Nuwambar da ya gabata.

Ministan Kwadago na gwamnatin tarayyar ne dai Dakta Chris Ngige ya bayyana hakan jim kadan bayan kammala wata tattaunawa da kungiyar malaman jami'o'in da yammacin ranar Litinin a garin Abuja.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel