Ina da niyyar yin aure amma lokaci nake jira - Nafisa Abdullahi

Ina da niyyar yin aure amma lokaci nake jira - Nafisa Abdullahi

- Nafisa Abdullahi ta ce tana da burin yin aure kamar kowanne mutum kuma nan gaba masoyanta za su sha labari

- Jarumar ta bayyana hakan ne a wani hira da ta yi BBC

- Shahararriyar jarumar dai ba ta bayyana takaimaiman lokacin da za ta yi auren ba

Shahararriyar jarumar nan ta dandalin shirya wasan Hausa, Nafisa Abdullahi ta ce tana da burin yin aure kamar kowanne mutum kuma nan gaba masoyanta za su sha labari.

Jarumar ta bayyana hakan ne a wani hira da ta yi BBC.

Ina da niyyar yin aure amma lokaci nake jira - Nafisa Abdullahi

Ina da niyyar yin aure amma lokaci nake jira - Nafisa Abdullahi
Source: UGC

Nafisa wacce tauraronta ke kan haskawa a masana’antar fin din ta fito a fina-finai da dama, sannan kuma tana daya daga cikin jarumai masu farin jini sosai.

Jarumar dai ba ta bayyana takaimaiman lokacin da za ta yi auren ba sai dai ta ce, "Aure kamar yadda nake fada kullum lokaci ne na ubangiji, amma kuma hade da niyya, ina da niyyar a raina amma lokacin nake jira."

KU KARANTA KUMA: Mambobin PDP 2,800 sun sauya sheka zuwa APC a mahaifar Buhari

Da aka tambaye ta mene ne sunan tauraron kuma ko daya ne daga cikin jaruman fim, sai ta yi dariya kuma ta ba da amsa kamar haka: "Ba shi da suna. Mai rabo ne kawai yana gefe."

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel