Ya zama dole Aisha Buhari ta yi bayanin abunda ya faru da masu hana ruwa gudu a Aso Rock - Fayose

Ya zama dole Aisha Buhari ta yi bayanin abunda ya faru da masu hana ruwa gudu a Aso Rock - Fayose

- Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose ya kalubalanci Aisha Buhari da ta yi wa yan Najeriya bayanin abunda ya faru da masu hana ruwa gudu da ta yi zargin suna hana gwamnatin mijinta tafiya yadda ya kamata

- Fayose ya soki Aisha akan kamfen da take yiwa maigidanta domin ya samu yin tazarce bayan ikirari da tayi lokuta da dama cewa wasu da ke tafiyar da gwamnatin mijinta sun sa ya gaza

- Yace maimakon asarar kudin jama’a wajen yiwa shugaban kasa kamfen, kamata yayi uwargidan shugaban kasar ta taimaka wa mijinta ya ar mulki

Wani tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose ya kalubalanci uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari da ta yi wa yan Najeriya bayanin abund ya faru da masu hana ruwa gudu da ta yi zargin suna hana gwamnatin ijinta tafiya yadda ya kamata.

Fayose a wani jawabi da ya saki a ranar Lahadi, 6 ga watan Janairu, ta hannun kakakinsa, Lere Olayinka ya soki Aisha akan kamfen da take yiwa maigidanta domin ya samu yin tazarce bayan ikirari da tayi lokuta da dama cewa wasu da ke tafiyar da gwamnatin mijinta sun sa ya gaza.

Ya zama dole Aisha Buhari ta yi bayanin abunda ya faru da masu hana ruwa gudu a Aso Rock - Fayose

Ya zama dole Aisha Buhari ta yi bayanin abunda ya faru da masu hana ruwa gudu a Aso Rock - Fayose
Source: UGC

Tsohon gwamnan ya bukaci sanin ko uwargidan shuaban kasar na kamfen ne da kudirin sake ganin yan Najeriya sun kuma wasu shekaru hudu a hannun masu hana ruwa gudu da ta zarga da hana gwamnatin mjinta ci gaba.

KU KARANTA KUMA: 2019: Atiku zai kai kamfen dinsa Kogi a yau, Litinin, 7 ga watan Janairu

Ya nemi sanin abunda Aisha Buhari za ta fada ma mata wadanda mazajensu da yaransu suka hada da matsala a hare-haren makiyaya ko wadanda mazajensu suka rasa ayyukansu a shekaru uku da suka gabata.

Yace maimakon asarar kudin jama’a wajen yiwa shugaban kasa kamfen, kamata yayi uwargidan shugaban kasar ta taimaka wa mijinta ya ar mulki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel