'Yan bindiga basu ji da dadi ba a hannun sojojin saman Najeriya a Zamfara

'Yan bindiga basu ji da dadi ba a hannun sojojin saman Najeriya a Zamfara

Rundunar Sojojin Sama ta ta ce sojojin ta na ‘Operation Idon Mikiya’ sun lalata wani sansanin ‘yan bindiga tare da kashe da dama daga cikin su a maboyar su dake cikin dazuzzukan jihar Zamfara dake a shiyyar Arewa maso yammacin Najeriya.

Ibikunle Daramola wanda shi ne Daraktan Yada Labarai na rundunar ya bayyana hakan a cikin wata sanarwar da fitar ya rabawa manema labarai inda ya ce dakarun su sun karkashe ‘yan bindigar ne kusa da Tsaunin garin Doumbourou, a Jihar ta Zamfara.

'Yan bindiga basu ji da dadi ba a hannun sojojin saman Najeriya a Zamfara

'Yan bindiga basu ji da dadi ba a hannun sojojin saman Najeriya a Zamfara
Source: Facebook

KU KARANTA: An cafke wani Fasto dake sayar da tikitin zuwa lahira

Legit.ng Hausa ta samu cewa an kai musu harin ne bayan da sojojin suka samu rahotannin sirri da bayanan inda mabuyar mahara din suke a kusa da tsaunin.

Masu leken asiri da na’urori sun tabbatar da hango maharani inda sukan rika taruwa a wani gida da ke kusa da tsaunin kafin su fita kai hare-hare. Harin farko ya lalata gidan tare da kashe mahara da dama.

A hari na biyu kuma da aka sake kaiwa, an kai shi ne a kan sauran maharan da suka tsere yayin da suke sake taruwa, inda aka sake bude musu wuta aka karkashe su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel