Bunkasa ayyuka: Rundunar sojin ruwa ta nada sabon mai magana da yawunta

Bunkasa ayyuka: Rundunar sojin ruwa ta nada sabon mai magana da yawunta

- Rundunar sojin ruwa ta nada Commodore Suleman Dahun, a matsayin sabon daraktan watsa labarai na rundunar

- Dahun ya yi karatunsa ne a jami'ar Maiduguri, inda ya kammala diriginsa a fannin koyon aikin jarida

- Commodore Dahun ya yi aiki a kusan kowanne bangaren aiki na rundunar sojin ruwa, kuma ya taba rike mukamin Daraktan watsa labarai a shelkwatar rundunar

Rundunar sojin ruwa ta nada Commodore Suleman Dahun, a matsayin sabon daraktan watsa labarai na rundunar. Daraktan tsare tsare na rundunar sojin ruwan, Rear Adm. O. Daji, ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a Abuja.

Dahun ya yi karatunsa ne a jami'ar Maiduguri, inda ya kammala diriginsa a fannin koyon aikin jarida.

"Babban jami'in rundunar ya kuma halarci kwas na mataimakin kakakin magana, a sansanin rundunar sojin sama na Royal A B, da ke Hilton, kasar Amurka, karkashin kungiyar JIOG, a shekarar 2016.

KARANTA WANNAN: Yanzu yanzu: Yadda hatsarin mota ya lakume rayuka 19 a jihar Bauchi

Bunkasa ayyuka: Rundunar sojin ruwa ta nada sabon mai magana da yawunta
Bunkasa ayyuka: Rundunar sojin ruwa ta nada sabon mai magana da yawunta
Asali: Facebook

"Haka zalika, ya samu horo na musamman akan kariyar aikin jarida a wuraren da ake tashin hankula, a cibiyar bayar da horo ta Hellenic Multi-National POSs, da ke Kilkis, kasar Greece, a shekarar 2016.

"Kuma ya halarci kwas kan watsa labarai karkashin JIAG, RAF, a Halton, (2017). Suleman mamba ne a kungiyar kwararru akan hulda da jama'a ta kasa," a cewar sanarwar.

Commodore Dahun ya yi aiki a kusan kowanne bangaren aiki na rundunar sojin ruwa, kuma ya taba rike mukamin Daraktan watsa labarai a shelkwatar rundunar sojin ruwan.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel