Yanzu yanzu: Yadda hatsarin mota ya lakume rayuka 19 a jihar Bauchi

Yanzu yanzu: Yadda hatsarin mota ya lakume rayuka 19 a jihar Bauchi

- Akalla mutane 19 ne suka gamu da ajalinsu a wani hatsarin mota da ya rutsa da su akan titin Gombe zuwa Darazo, a jihar Bauchi.

- Rahotanni sun bayyana cewa motar da fasinjojin cikinta suka mutu, na gudun wuce sa'a lokacin da hatsarin ya afku

- Hukumar FRSC ta bayyana cewa motar kirar Hummer Bas, mai dauke da mutane 18, ta yi karo da wata babbar tirela ne akan hanyarsu ta zuwa jihar Kano daga Gombe

Rahoton da Legit.ng ta samu daga shafin Punch, na nuni da cewa akalla mutane 19 ne suka gamu da ajalinsu a wani hatsarin mota da ya rutsa da su akan titin Gombe zuwa Darazo, a jihar Bauchi. Hatsairin ya afku ne a yammacin ranar Alhamis.

Wani jami'in hukumar kiyaye hadurra ta kasa FRSC a Darazo, wanda ya bukaci a sakaya sunansa kasancewar rashin samun umurnin zantawa da manema labarai, ya ce motar da fasinjojin cikinta suka mutu, na gudun wuce sa'a lokacin da hatsarin ya afku.

Ya ce matafiyan na kan hanyarsu ne zuwa jihar Kano daga jihar Gombe, a lokacin da motar ta yi katantanwa, tare da kashe dukkanin fasinjojin dake cikinta, in banda mutane biyu da suka samu munanan raunuka.

KARANTA WANNAN: Yanzu yanzu: Buhari ya bada umurnin hukunta Pinnick kan zargin sace biliyoyin kudin NFF

Yanzu yanzu: Yadda hatsarin mota ya lakume rayuka 19 a jihar Bauchi

Yanzu yanzu: Yadda hatsarin mota ya lakume rayuka 19 a jihar Bauchi
Source: Original

A cewar sa, an garzaya da su babban asibitin Darazo, da ke karamar hukumasr Darazo, jihar Bauchi, don basu kulawar likita cikin gaggawa, inda ya kara da cewa akwai gawarwaki 19 da aka kaisu dakin ajiye gawa na babban asibitin Darazo.

Sain dai da yake tabatar da faruwar hatsarin ga wakilin jaridar Punch a wayar salula, shugaban sashen ayyuka na hukumar FRSC, reshen jihar Bauchi, Paul Guah ya ce sun samu rahoton mutuwar mutane 13 ne a cikin hatsarin.

Guah, mataimakin kwamandan rundunar ya ce, motar kirar Hummer Bas, mai dauke da mutane 18, ta yi karo da wata babbar tirela ne akan hanyarsu ta zuwa jihar Kano daga Gombe.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel